Da duminsa: 'Yan bindiga sun sace mutane 60 bayan kona gidaje a Ruwan Tofa a Zamfara
- Yan bindiga sun kai hari garin Ruwan Tofa da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara
- Bata-garin sace a kalla mutum 60 bayan kwace dukiyoyi da kona gidaje da shaguna da motoccin al'umma
- An yi kokarin ji ta bakin rundunar yan sandan jihar Zamfara kan batun amma ba a yi nasara ba
'Yan bindiga sun afkawa jama'ar garin Ruwan Tofa da ke karamar hukumar Maru a jihar Zamfara inda suka sace a kalla mutum 60, suka kona rabin garin tare da sace kayan abinci da wasu dukiyoyi, BBC ta ruwaito.
Hakan na zuwa ne yayin da gwamnatin jihar ta saka dokar hana fita a garin Jangebe sakamakon zanga-zangar da matasa suka yi na nuna bacin ransu kan sace mutane da kashe-kashe da ta koma tarzoma.
DUBA WANNAN: Allah ya yi wa ango rasuwa kwana ɗaya bayan ɗaurin aurensa
Wani mazaunin garin da aka boye sunansa ya ce, "Abin ya mana nauyi, ko jiya da shekaranjiya ma an kawo mana hare-hare. Sun kona mana shaguna, motocci da gidaje, kusan rabin garin suka kona."
Ya kara da cewa rai bai salwanta ba amma yan bindigan sun harbi wani mutum da yanzu haka ya ke asibiti a kwance yana jinya.
Ya cigaba da cewa sun tafi da yara da mata masu yawa har ma da wakilin mai garin da iyalansa.
Wani daban da lamarin ya shafa ya ce an sace mutum 15 daga gidansa da suka hada da mata da yara sun kuma kwashe masa buhunnan dawa 90.
"Mun nemi taimakon jami'an tsaro har sau biyu amma ba su zo ba, don haka muka tsere daga garin," a cewarsa.
BBC ta yi yunkurin ji ta bakin rundunar yan sandan jihar Zamfara amma hakan ya ci tura.
A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.
NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.
Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.
Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.
Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.
Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.
Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu
Asali: Legit.ng