'Yan bindiga sun bamu lambobin waya, sun ce za su zo neman aurenmu, 'Yammatan Jangebe
- 'Yammatan makarantar Jangebe da aka saki sun sanar da yadda 'yan bindiga suka basu lambobin wayoyinsu
- Sun bayyana cewa masu garkuwa da mutanen sun sha alwashin zuwa har gidajensu neman aurensu don suna sonsu
- Dalliban sun sanar da yadda 'yan bindigan suka basu shawarar su yi watsi da karatu su yi aurensu kawai
'Yan bindigan da suka sace 'yammatan makarantar Jangebe sun basu lambobin wayarsu bayan sakinsu da suka yi ranar Talata tare da yin alkawarin za su zo wurin iyayensu neman aurensu.
'Yanmatan da suka zanta da Daily Trust sun ce wadanda suka sace su sun sanar dasu cewa suna son su kuma sun yi alkwarin tuntubarsu ta waya domin jin ko sun samu karbuwa.
Wata daliba mai suna Hassatu Umar Anka, ta ce wadanda suka sace su sun basu shawarar su bar makaranta kawai su yi aurensu.
KU KARANTA: Bidiyo: Garkuwa da 'yan makaranta da 'yan bindiga ke yi karamin laifi ne, Sheikh Gumi
"A lokacin da suka zo sakinmu, wasu sun fara nuna wasu daga cikinmu inda suke cewa muna son waccan, muna son aurenku idan kun amince da tayin soyayyarmu. Ku daina bata lokacinku wurin karatun," tace.
Ta ce 'yan bindigan na mugun tsoron sojoji domin duk lokacin da jiragen yaki suka je shawagi a saman, a guje suke neman wurin buya.
"Suna kiran jiragen sojojin da "Shaho" kuma idan suka ga ko daya ne sai su ce mu boye a koguna ko bishiyoyi. Suna masifar tsoronsu," ta kara da cewa.
KU KARANTA: Mayakan ISWAP sun kaiwa kwamandan Operation Lafiya Dole farmaki a Borno
A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule lamido, ya ce Salihu Tanko Yakasai, tsohon hadimin Ganduje na jihar Kano, yafi Femi Adesina da Garba Shehu jarumta.
An kama Salihu a ranar Asabar bayan ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi murabus sakamakon yawaitar rashin tsaro a kasar nan.
Labarin damke shi da aka yi ya karade gari yayin da Ganduje ya sanar da cewa ya sallame shi daga aiki, Daily Trust ta wallafa. A yayin martani a wata takardar da Lamido ya fitar ranar Litinin, ya ce Salihu jarumi ne kamar mahaifinsa wanda ya tsaya tsayin daka kuma ya gagari miyagun shugabanni.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng