Manoman albasa a jihar Kano sun fara shiga damuwa kan yajin aikin kai kaya Kudu
- Wasu 'yan kasuwar albasa a jihar Kano sun fara shiga damuwa dalilin shiga yajin aikin dillalai
- 'Yan kasuwan sun nuna damuwarsu kan yadda farashin alabasa ya fara muni a kasuwarsu
- Sun kuma bayyana cewa, farashin albasan ya nuna alamun tabarbarewar kasuwancin albasa a jihar
Wasu manoman albasa da ‘yan kasuwarta a jihar Kano suna kukan kan tasirin katange kai kayan abinci zuwa yankin kudancin kasar nan.
Don nuna rashin amincewa da harin da aka kai wa ‘yan kasuwa a wasu Jihohin Kudu Maso Yamma, kungiyar Hadakar Dillalan Kayan Abinci da Shanu na Najeriya (AUFCDN) ta fara yajin aiki.
Wannan ya haifar da hauhawar farashin kayayyakin masarufi a kudu amma a arewa, farashin na ta faduwa warwas.
KU KARANTA: Wike ya sasanta gwamnan jihar Benue da na Bauchi kan batun makiyaya
A ranar Talata, Daily Trust ta ziyarci Kasuwar Albasa ta Gun-Dutse da ke karamar Hukumar Dawakin Kudu a Jihar Kano don ganin yadda ’yan kasuwar ke jure zafin yajin aikin.
Wasu daga cikinsu sun ce kafin zanga-zangar, galibi suna jigilar akalla motoci 20 zuwa yankin kudancin kasar a kullum amma yajin aikin ya shafe su sosai.
Babban buhun albasa, wanda ake siyarwa akan kudi N35,000 'yan makonnin baya kuma ya haura N70,000 a lokacin tsananin rashin albasar a shekarar data gabata, yanzu ana siyar dashi akan kudi N7,000.
KU KARANTA: Munguno: Muna da rahotannin sirri na wadanda ke cin gajiyar rashin tsaro
A wani labarin, Yajin aikin da dillalan kayan abinci suka shiga na kungiyar Hadin kan Dillalan Kayan Abinci da Shanu (AUFCDN), ya janyo hau-hawan farashin kayayyaki a yankin kudancin Najeriya, a cewar rahoton Daily Trust.
Kungiyar ta AUFCDN wacce bangare ne na kungiyar kwadago ta kasa wato (NLC), ta shiga yajin aikin ne a ranar Alhamis biyo bayan karewar wa'adin da ta bai wa Gwamnatin Tarayya na kwana bakwai da ta biya mata bukatunta.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng