Wasu Yan Ta'adda Sun Kashe Mutum daya, sun yi awon gaba da matafiya a Osun

Wasu Yan Ta'adda Sun Kashe Mutum daya, sun yi awon gaba da matafiya a Osun

- Wasu Yan Ta'adda Sun Kashe Mutum daya, sun yi awon gaba da matafiya a Osun.

- Wani mutum yace yaji karar harbe harbe daga kauyen su dake kusa da wajen

- An tabbatar da aukuwar lamarin ranar talata da daddare

A ranar Talata da daddare, tsoro ya hana bin hanyar Osogbo/Ibokun saboda labarin da aka samu wasu yan ta'adda sunyi awon gaba da matafiya akan hanyar.

Jaridar Thenation ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 7:30pm na dare a kusa da kauyen Aje Bamidele yankin karamar hukumar Obokun ta jihar Ogun.

KARANTA ANAN: Dan adaidaita sahu ya mayar da N2.8m ga fasinja bayan ya tsinci kudin a cikin adaidaitarsa

Wani mazaunin garin da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyanawa thenation cewa "Munji karar harbi sannan kuma munga motocin dake bin hanyar na dawo wa. Na sami labarin sun kashe mutum daya kuma sunyi awon gaba da wasu da dama"

Wasu Yan Ta'adda Sun Kashe Mutum daya, sun yi awon gaba da matafiya a Osun
Wasu Yan Ta'adda Sun Kashe Mutum daya, sun yi awon gaba da matafiya a Osun Hoto: rfi.fr
Asali: UGC

KARANTA ANAN: Wata Kotu Ta Yankewa Wani Mutumi Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya

Kwamishinan Amotekun a jihar ya tabbatar da aukuwar lamarin, yace "Yan bindigan sun sace mutum daya sannan sun yi awon gaba da matafiya, zuwa yanzun bamu tabbatar da yawan su ba"

Ya kara da cewa "Anyi amfani da bindiga kirar AK-47 a wajen. Muna cigaba da kokarin ceto wadan da suka sace"

A wani labarin kuma Kungiyar Kwadugo NLC ta Shirya Zanga Zanga akan Shirin Yan Majalisu Na Chanja Mafi Karancin Albashi

Ayuba Waba shugaban Kungiyar ya bayyana haka bayan wani taron gaggawa a Abuja

Zamuyi zanga zanga akan shirin yan majalisu na chanja ma mafi karancin albashi tsari, cewar yan kwadago

Ahmad Yusuf dalibi ne mai neman ilmi. Ya karanci Bsc Mathematics a jami'ar kimiyya da fasaha dake garin wudil, jihar Kano.

Za'a iya samunsa a facebook facebook.com/Ahmed.yusuf.dabai

Asali: Legit.ng

Online view pixel