Wata Kotu Ta Yankewa Wani Mutumi Hukuncin Kisa Ta Hanyar Rataya
- Wata kotu dake zamanta a Abekuta ta yankewa wani matashi hukuncin kisa
- Matashin ya kashe wani jariri dan kimanin shekaru biyu kacal
- Matar da aka aikatawa dan ta wannan aika aika ta bada shaidar duk abinda ya faru
A ranar Talatan nan, Wata kotu dake zamanta a Abekuta Babban birnin Jihar Ogun ta yankewa wani mutumi mai suna Mohammed Ibrahim hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kamashi da laifin kisan wani jariri dan shekara biyu.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Alkalin kotun, Mai Shari'a Ayokunle Rotimi-Balogun, ya kuma kama mutumin da hannu dumu dumu wajen kokarin kashe wata mata Rabi Yakubu.
KARANTA ANAN: EFCC ga 'yan Najeriya: Kada ku sake taya Bawa murnar zama shugaban EFCC
Wacce ta gurfanar dashi, Mrs Oluwabumi Akinola, ta bayyana ma kotun cewa ranar 12 ga Afrilu, 2014 a garin Ofada, Mrs Yakubu na dauke da jaririnta dan kimanin shekara biyu, zuwa wurin da za ta biya ma kanta bukata cikin daji.
KARANTA NAN: Daga karshe Gwamna Matawalle ya bayyana wadanda ke daukar nauyin 'yan ta'adda a Zamfara
"Lokacin da ta isa wajen ta ajiye jaririn nata a kasa domin samun dama yadda yakamata, ba zato ba tsammani sai Ibrahim ya farmake ta da wuka yana kokarin cire mata kai"
"Mai karar tace tayi kokawa da ibrahim har tasamu ta tsere masa ba tare da ta dauki jaririn ta ba. Da ibrahim ya fahimci bai samu nasara wajen cire mata kai ba wanda yake bukata don ya siyar, sai ya cire kan jaririn nata"
Akintola ta kara ma kotu jawabi da cewa matar da take karewa ta yi cikakken bayani akan aukuwar lamarin, tace abinda yaso shine ya cire mata kai.
A wani labarin kuma Allah ya yi wa kanin Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi rasuwa
Ya rasu bayan rashin lafiya da yayi fama da ita a wani asibiti da ke Abuja
Za a yi jana'izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a masallacin kasa
Asali: Legit.ng