Yanzun-nan: Jihohin kudu 6 sun yi martani a kan hana abinci daga arewa, sun bayyana matakin dauka na gaba
- Dakatar na kai kayan abinci zuwa Kudancin Najeriya ya haifar da martani daga gwamnatocin jihohin kudu
- Enugu, Cross River, Ondo da wasu jihohi uku sun ce daga karshe ci gaban zai amfani yankin kudu ne
- Jihohin sun ce suna kara himma don bunkasa kayan abincinsu na gida da kuma kiwon dabbobi domin rage dogaro da wani tushe na waje
Wasu gwamnatocin jihohin kudu da manoma sun mayar da martani game da shawarar da dillalan shanu da na kayan abinci na arewa suka yanke na dakatar da kai kayansu jihohin kudu.
Jihohin kudu shida, wadanda suka hada da Lagos, Cross River, Akwa Ibom, Delta, Enugu da Ondo, sun yi watsi da katangewar, suna masu cewa wata dama ce ga kudu ta bunkasa kayan abinci da dabbobin ta, jaridar The Punch ta ruwaito.
Ku tuna cewa dillalan shanu da kayan abinci a karkashin hadaddiyar gamayyar kungiyar nan ta Kayan Abinci da Dillalan Shanu na Najeriya a ranar Alhamis, 25 ga watan Fabrairu, sun dakatar da kai kayan abinci zuwa kudu.
KU KARANTA KUMA: Daga karshe Gwamna Matawalle ya bayyana wadanda ke daukar nauyin 'yan ta'adda a Zamfara
Sun ce sun fara yajin aikin ne saboda gazawar gwamnatin tarayya na biyan bukatunsu, wadanda suka hada da biyan diyya na asarar rayuka da dukiyoyi yayin zanga-zangar #EndSARS da rikicin kabilanci da ya faru a kasuwar Shasha da ke Ibadan.
Don aiwatar da yajin aikin, kungiyar ta hana mambobin jigilar dabbobi da abinci daga arewa zuwa yankin kudancin kasar.
Kungiyar ta dage kan cewa ba ta janye yajin aikin ba.
Martanin gwamnatocin jihohi
Akin Olotu, babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu, kan harkokin noma da cinikin kayan gona, ya bayyana takunkumin a matsayin ci gaba mai kyau.
Ya ce bude ido ne don amfani da damar da kudu ta samu a harkar noma.
A nata martanin, gwamnatin jihar Delta ta ce takunkumin ba ya wakiltar hadin kan Najeriya.
Gwamnatin jihar, ta ce tana ci gaba da himma wajen karfafa noman abinci na cikin gida.
Da yake maida martani, gwamnatin jihar Cross River ta ce shingen ba zai dawwama ba, inda ta kara da cewa takunkumin daga baya zai cutar da manoman musamman wadanda ke samar da kayayyakin da ke lalacewa.
Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta ce tana aiki don tabbatar da cewa kashi 80% na abin da ake ci an samar da shi a jihar kamar yadda gwamnatin jihar ta Enugu ta ce za ta tabbatar jihar ta wadatar da samar da isasshen abinci nan gaba kadan.
KU KARANTA KUMA: Ta'addanci: NDLEA ta kwace bindigogi 27 daga hannun wasu mutane a jihar Neja
A nata bangaren, gwamnatin jihar Legas ta ce ba a sanar da ita a hukumance ba game da duk wata shawarar janye kayan zuwa jihar.
Kwamishinan yada labarai da dabaru na jihar Legas, Gbenga Omotosho, shi ma ya ce jihar ba ta jin wani tasiri na karancin abinci.
Duk da haka, Omotosho ya ce Legas ta riga ta shirya don gaba ta bangaren samar da abinci.
A wani labarin, Kungiyar dattawan Arewa (ACF), ta yi kira ga shugabannin kungiyar Hadin Kan Abinci da Dillalan Shanu da su janye takunkumin da suka sanya na kai kayan abinci daga arewa zuwa kudu, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban ACF na kasa, Cif Audu Ogbe, a cikin wata sanarwa da ya fitar a Kaduna, ya ce: “Najeriya ba ta yaki da kanta kuma irin wannan tsattsauran mataki bai da amfani, amma zai kara dagula matsalolin tattalin arziki da siyasa da kasarmu ke fuskanta ne a yau.”
“Kungiyar ta ACF, ta damu da damuwar yan Najeriya dangane da shawarar da Hadaddiyar Kungiyar Abinci da dillalan shanu suka yanke na dakatar da zirga-zirgar abincin da ake bukata daga arewa zuwa kudu."
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng