Allah ya yi wa kanin Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi rasuwa

Allah ya yi wa kanin Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi rasuwa

- Kanin gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu ya rasu

- Ya rasu bayan rashin lafiya da yayi fama da ita a wani asibiti da ke Abuja

- Za a yi jana'izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar a masallacin kasa

Shehu Bagudu, kanin gwamnan jihar Kebbi, Gwamna Atiku Bagudu ya rasu.

Mai bada shawara na musamman ga gwamnan a fannin yada labarai, Yahaya Sarki, ya sanar da hakan a wata takarda da ya fitar, The Nation ta wallafa.

Ya ce dattijon mai shekaru 55 ya rasu a yammacin Talata a wani asibiti da ke zaman kansa a Abuja bayan gajeriyar rashin lafiya.

Za a yi jana'izarsa a ranar Laraba, 3 ga watan Maris na 2021 a masallacin kasa da ke Abuja da karfe 11 na safe.

KU KARANTA: Gara mu yi asarar kayan, 'Yan kasuwan arewa sun yi martani kan hana kudu kayan abinci

Allah ya yi wa kanin Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi rasuwa
Allah ya yi wa kanin Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi rasuwa.Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

KU KARANTA: Yanzu haka, mayakan Boko Haram sun budewa Dikwa da Gajiram wuta

A wani labari na daban, daya daga cikin dalibai 279 na GGSS Jangebe dake jihar Zamfara da 'yan bindiga suka sako bayan sun sace su a ranar Juma'a ta bayyana yadda 'yan bindigan da suka sacesu suka bukaci addu'o'insu.

Kamar yadda ta shaidawa NAN a gidan gwamnatin jihar Zamfara dake Gusau a ranar Talata, tace sun bukaci su tayasu da addu'ar dacewa da canja hali daga munanan dabi'unsu zuwa masu kyau.

Kamar yadda tace, "Sun cutar damu har da kiranmu da munanan sunaye, sun yi yunkurin kashe mu, amma daga baya sun bukaci mu tayasu da addu'a don su zama mutanen kirki kuma mu koya musu turanci."

"Sun yi yunkurin yi mana fyade, amma shugabansu ya tsawatar musu, har kasa suke zuba mana a abinci kuma su umarci mu haka rami da hannunmu don mu samu ruwa," a cewarta.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: