Yanzu Yanzu: Obasanjo, Saraki da sauran jiga-jigan PDP sun shiga labule yayinda tseren zaben 2023 ke kara zafi

Yanzu Yanzu: Obasanjo, Saraki da sauran jiga-jigan PDP sun shiga labule yayinda tseren zaben 2023 ke kara zafi

- Tawagar sulhu ta PDP karkashin jagorancin Saraki ta karkata akalarta ga tsohon shugaban kasar Najeriya, Obasanjo

- Saraki da sauran mambobin kungiyar suna ganawa da tsohon shugaban a Abeokuta

- Babu cikakken bayani game da wannan ganawar a daidai lokacin kawo wannan rahoton

A yanzu haka, Bukola Saraki, shugaban majalisar dattawa ta takwas yana cikin ganawar sirri da tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo, a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun.

Ayarin Saraki sun isa dakin karatun Olusegun Obasanjo OOPL, Abeokuta da tsakar ranar Talata, 2 ga watan Maris.

Kai tsaye bayan isowarsa, Saraki wanda shine shugaban kwamitin sulhu na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ya shiga wata ganawar sirri da Obasanjo a gidansa na Pent House.

Yanzu Yanzu: Obasanjo, Saraki da sauran jiga-jigan PDP sun shiga labule yayinda tseren zaben 2023 ke kara zafi
Yanzu Yanzu: Obasanjo, Saraki da sauran jiga-jigan PDP sun shiga labule yayinda tseren zaben 2023 ke kara zafi Hoto: Kehinde Akinyemi, hadimin labaran Olusegun Obasanjo
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: ACF ga hukumomin tsaro: A binciki Matawalle don gano wadanda suka sace 'yan matan makarantar Jangebe

Kehinde Akinyemi, hadimin Obasanjo kan harkokin yada labarai ya aika wa Legit.ng hoton maigidan nasa tare da tsohon shugaban majalisar dattawan yayin da suka gaisa cikin nishadi.

A cewar hadimin labaran, mambobin tawagar Saraki sun hada da jiga-jigan PDP kamar su Ibrahim Shehu Shema, Ibrahim Hassan Dankwanbo, Liyel Imoke, Mulikat Akande Adeola, da Olagunsoye Oyinlola.

Obasanjo, wanda ya yi wa'adin mulkin sa guda biyu a matsayin shugaban kasa a karkashin PDP, ya yayyaga katinsa na zama mambar jam’iyyar a bainar jama'a a lokacin da za a fara zaben 2015.

Tsohon shugaban kasar ya kuma lamuncewa Shugaba Muhammadu Buhari a zaben 2015.

KU KARANTA KUMA: Bayan wata uku da sace su: Na ga mahaifina da yayata a wurin yan bindiga, dalibar Jangebe da aka sako

A wani labari na daban, Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattawa ta amince da nadin Dr. Halilu Shaba Ahmad a matsayin darektan hukumar NASRDA.

Punch ta ce Halilu Shaba Ahmad ne ake sa rai zai jagoranci aikin wannan hukuma da ke kula da nazari da binciken harkokin sama jannati ta Najeriya.

Jaridar ta rahoto cewa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, ya karanto wasikar shugaban kasar a ranar Talata, 2 ga watan Maris, 2021.

Amma, ya janye goyon bayansa ga Shugaba Buhari kafin zaben 2019 sannan daga baya ya ce ba zai sake shiga siyasa ba.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel