ACF ga hukumomin tsaro: A binciki Matawalle don gano wadanda suka sace 'yan matan makarantar Jangebe

ACF ga hukumomin tsaro: A binciki Matawalle don gano wadanda suka sace 'yan matan makarantar Jangebe

- Kungiyar ACF ta bukaci hukumomin tsaro da su binciki Gwamna Bello Matawalle a kan satar yaran makarantar Jangebe a jihar Zamfara

- Hakan ya biyo bayan kalmar da aka alakanta da gwamnan ne inda yace ya san wadanda suka sace yaran, sannan cewa idan ya bayyana su yan Najeriya za su sha mamaki

- ACF ta bayyana kalaman da gwamnan ke yi a matsayin sakin zance inda ta kalubbalance shi da lallai ya bayyana ko su wanene

Kungiyar Arewa ACF, ta yi kira ga hukumomin tsaro da su binciki gwamnan jihar ta Zamfara, Bello Matawalle sannan su sa ya bayyana asalin wadanda suka sace 'yan matan makarantar Jangebe 317.

Kungiyar ta arewacin kasar ta bayyana cewa, idan har Gwamna Matawalle bai bayyana sunayen wadanda suka sace 'yan matan makarantar ba, ya kamata a dauki shi a matsayin wanda ke bada hadin kai wajen aikata laifin satar mutane.

An ruwaito Gwamna Matawalle ya fada wa Sarakuna 17 wadanda suka kai masa ziyarar jaje kan sace ’yan matan makaranta 317, cewa ya san wadanda suka sace su kuma idan ya bayyana asalinsu, ‘yan Najeriya za su firgita.

ACF ga hukumomin tsaro: A binciki Matawalle don gano wadanda suka sace 'yan matan makarantar Jangebe
ACF ga hukumomin tsaro: A binciki Matawalle don gano wadanda suka sace 'yan matan makarantar Jangebe Hoto: @vanguardngrnews
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin Yobe ta rufe dukkanin makarantun kwana a fadin jihar

ACF a wata sanarwa da ta fitar a ranar Talata ta hannun Shugabanta na Kasa kuma tsohon Ministan Noma, Cif Audu Ogbe ya ce, dole ne Gwamna Mutawalle ya daina kunyata arewa da kasar da maganganun sakaci kan babban lamari kamar sace yaran makaranta.

A cewar Ogbe, “Kungiyar ACF ta yi mamakin bayanin da aka ce Gwamnan jihar Zamfara, Bello Mutawalle ne ya fade shi.

“An ruwaito a kafafen yada labarai cewa Gwamnan ya fada wa Sarakuna 17 da suka kai masa ziyarar jaje kan sace’ yan mata ’yan makaranta 317 daga Makarantar Sakandaren’ Yan Mata ta Gwamnati Jangebe a Talata Mafara cewa ya san asalin masu garkuwar kuma idan ya bayyana su waye , Yan Najeriya zasuyi mamaki.

“Muna rokon gwamnan da ya tona asirin su ya kuma bari yan Najeriya su kadu ko ma sama ta fadi.

“Muna kuma rokon hukumomin tsaro da su yi wa gwamnan tambayoyi a kan sunayen masu laifi da yake kokarin boyewa. Idan ya ƙi bayyana sunayensu, dole ne a ɗauke shi a matsayin mai hannu cikin aikata laifin satar mutane.

“ACF ta ji kunya saboda yawan sace-sacen yara musamman na ‘yan makaranta da ke yaduwa kamar wutar daji a duk fadin arewa.

KU KARANTA KUMA: Bayan wata uku da sace su: Na ga mahaifina da yayata a wurin yan bindiga, dalibar Jangebe da aka sako

“Mutanen da suke kan mukamai wadanda za su taimaka mana daga wannan kangin kamar Gwamna Mutawalle dole ne su daina kunyata arewa da kasar da kalamai na gangaci a kan lamari mai mahimmanci kamar sace yaran makaranta.

“Jihar Zamfara da arewa suna bayan sauran yankunan kasar a ci gaban ilimi. Sace-sacen daliban makaranta a arewa zai kara munanawa da sanya rashin yarda da yanayin ilimin Arewa.

A wani labarin, wasu bayin Allah sun sake rasa ransu a hannun yan ta’adda a Najeriya.

A wannan karon, yan bindigan sun kashe kimanin mutane 10 a Zangon Kataf da ke karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna.

Kwamishinan tsaron cikin gida, Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel