Na Rasa Inda Zansa kaina Saboda Farin Ciki, A Cewar Wani Mahifi Bayan Sako Yan Matan Jengebe

Na Rasa Inda Zansa kaina Saboda Farin Ciki, A Cewar Wani Mahifi Bayan Sako Yan Matan Jengebe

- An sako yan matan da aka kama a makarantar kwana ta mata dake Jangebe

- Jama'a a garin Jangebe sun barke da murna bayan dawowar daliban da yan ta'adda suka sace.

- Wasu daga cikin wanda suka kama mu sunce suna neman mu da aure

Mahaifin biyu daga cikin yan mata dalibai 279 na makarantar sakandiren gwamnati, Jangebe, Jihar Zanfara da aka sace a kwanakin baya, ya nuna tsantsar farin cikin sa da cewa, Babu wata kalma da zata iya nuna irin farin cikin da yake ciki bayan sakin daliban wadan yayan sa biyu ke ciki. An saki Daliban ne da sanyin safiyar Talata.

KARANTA ANAN: Babbar magana: Binciken Bola Tinubu ya yi zurfi, EFCC ta na bin bayanan kadarorin da ya mallaka

Mutumin mai suna Rilwanu Mohammed Jangebe, ya bayyana tsantsar farin cikinsa akan sakin daliban da akayi.

Na Rasa Inda Zansa kaina Saboda Farin Ciki, A Cewar Wani Mahifi Bayan Sako Yan Matan Jengebe
Na Rasa Inda Zansa kaina Saboda Farin Ciki, A Cewar Wani Mahifi Bayan Sako Yan Matan Jengebe
Source: Instagram

KARANTA ANAN: Makuden kudaden fansa na karfafawa masu garkuwa da mutane guiwa, Buhari

Ya kuma shaidawa kafar yada labarai ta BBC, duk da cewa gwamnatin jihar bata sanar dasu sakin yaran nasu ba amma sun samu wannan labari mai dadi da misalin karfe 4 na safiya daga wani dan uwansa dake aiki a gidan gwamnati.

Duk da kasancewar yana cikin tsantsar murna, Rilwanu yace an barke da murna a garin Jangebe bayan an sanar da sakin yan makarantar da Gwamnati tayi.

A safiyar Ranar Jumu'a ne wasu yan bindiga suka kai hari makarantar mata dake Jangebe, karamar hukumar Talatan Mafara a jihar Zamfara inda sukayi awon gaba da Dalibai guda 279.

Saidai a labarin da muke samu yau, an saki Daliban da aka sace.

A wani labarin kuma Gwamnan Bauchi yayi kira ga al'unar mazabar dogara da kada subari a yaudare su.

Gwamnan yayi wannan jawabi ne lokacin daya kai ziyarar ganin aikin hanyoyin dake gudana yankin.

Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi yayi kira ga al'umma da su bashi hadin kai.

Source: Legit.ng

Online view pixel