Babbar magana: Binciken Bola Tinubu ya yi zurfi, EFCC ta na bin bayanan kadarorin da ya mallaka

Babbar magana: Binciken Bola Tinubu ya yi zurfi, EFCC ta na bin bayanan kadarorin da ya mallaka

- Hukumar EFCC ta na fadada bincike a kan tsohon Gwamnan Legas, Bola Tinubu

- EFCC ta aika takarda, ta na neman bayanai kan kadarorin Asiwaju Bola Tinubu

- Abdulrasheed Bawa ya sa hannu a takardar a lokacin ya na rike da ofishin Legas

Hukumar EFCC mai yaki da masu yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon-kasa ta zurfafa bincike a kan babban jigon jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Tinubu.

The Peoples Gazette ta rahoto cewa EFCC ta rubuta takarda zuwa ga hukumar CCB mai bibiyar kadarori, ta nemi a bata takardun tsohon gwamnan naLegas.

Jaridar The Peoples Gazette ta samu ganin wasikar da hukumar EFCC ta rubuta zuwa ga CCB.

Rahotannni sun tabbatar EFCC ta fara binciken Bola Tinubu ne tun a shekarar 2020 da ta gabata, kafin tsige Ibrahim Magu daga kujerar shugaban hukumar.

KU KARANTA: Apara ya na karar Tinubu a kotu bisa zargin da ke kan kamfanin Alpha-Beta

Wasikar mai lamba ta CR/3000/EFCC/LS/Vol4/322, ta fito ne a ranar 6 ga watan Nuwamba, 2020, wanda ya sa hannu a kan takardar shi ne Abdulrasheed Bawa.

A wancan lokaci, Bawa ya na rike da mukamin shugaban babban ofishin EFCC na yankin Legas. A watan jiya aka tabbatar da shi a matsayin shugaban hukumar.

Wasikar ta na cewa: “A game da wannan batu, mu na neman ku gabatar wa hukumar da duk wasu bayanai da ake nema a kan Bola Ahmed Adekunle Tinubu.”

EFCC ta dogara ne da sassa na 38(1) da (2) na dokar 2004 da ta kafa hukumar a wajen neman bayanan.

Binciken Bola Tinubu ya fara zurfi, EFCC ta fara bin bayanin kadarorin da ya mallaka a Duniya
Bola Tinubu Hoto: punchng.com
Source: UGC

KU KARANTA: Masoya su na so tsohon Shugaba Jonathan ya shiga takara a zaben 2023

Jaridar ta ce ta yi yunkurin tuntubar mai magana da yawun EFCC, Wilson Uwujaren, amma abin bai yiwu ba. Sai dai wani jami’i ya tabbatar da sahihancin takardar.

Tun a 2019 ku ka ji cewa wasu kungiyoyi kusan 150 da ke fafutukar yaki da rashin gaskiya sun nemi a binciki wasu kamfanoni wanda su ka hada har da Alpha Beta.

Kungiyoyin da ke yakar cin hanci da rashawa a Najeriya sun hurowa Hukumar EFCC wuta cewa ta gudanar da bincike game da badakalar da ake zargin kamfanonin da su.

Ana zargin tsohon gwamnan na jihar Legas, Bola Tinubu ne ya mallaki kamfanin Alpha Beta.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel