'Yan bindigan da suka sace mu sun bukaci mu dinga musu addu'a, 'Yammatan Jangebe

'Yan bindigan da suka sace mu sun bukaci mu dinga musu addu'a, 'Yammatan Jangebe

- Hunainatu Abubukar, daya daga cikin daliban GGSS Jangebe dake Zamfara, ta ce wadanda suka yi garkuwa dasu sun bukaci addu'arsu

- A cewar ta, 'yan bindigan sun bukaci su yi musu addu'ar samun shiriya da komawa tafarkin gaskiya da tsoron Allah

- Ta sanar da manema labarai hakan ne a ranar Talata, bayan an sako dalibai 279 wadanda aka sace tun ranar Juma'a

Daya daga cikin dalibai 279 na GGSS Jangebe dake jihar Zamfara da 'yan bindiga suka sako bayan sun sace su a ranar Juma'a ta bayyana yadda 'yan bindigan da suka sacesu suka bukaci addu'o'insu.

Kamar yadda ta shaidawa NAN a gidan gwamnatin jihar Zamfara dake Gusau a ranar Talata, tace sun bukaci su tayasu da addu'ar dacewa da canja hali daga munanan dabi'unsu zuwa masu kyau.

Kamar yadda tace, "Sun cutar damu har da kiranmu da munanan sunaye, sun yi yunkurin kashe mu, amma daga baya sun bukaci mu tayasu da addu'a don su zama mutanen kirki kuma mu koya musu turanci.

KU KARANTA: Satar 'yan makaranta: Wasu jama'a ne ke yunkurin tozarta wannan gwamnatin, Sirika

'Yan bindigan da suka sace mu sun bukaci mu dinga musu addu'a, 'Yammatan Jangebe
'Yan bindigan da suka sace mu sun bukaci mu dinga musu addu'a, 'Yammatan Jangebe. Hoto daga @Vanguardngrnews
Source: Twitter

"Sun yi yunkurin yi mana fyade, amma shugabansu ya tsawatar musu, har kasa suke zuba mana a abinci kuma su umarci mu haka rami da hannunmu don mu samu ruwa," a cewarta.

A cewar Hanainatu tana da burin komawa Kaduna, inda ta fito, don ta cigaba da karatu ta zama lauya kamar yadda ta dade tana buri.

"Wasu daga cikin 'yan bindigan sun bukaci mu auresu amma babu wacce ta tanka musu sai suka ce zasu samu masu manyan idanu su kashe."

A cewarta duk da da daddare ne aka mayar dasu makarantarsu, tsaf za ta iya gane inda aka kaita wurin kuma za ta gane fuskokinsu.

A cewarta daya daga cikin daliban ta ga babanta da akayi garkuwa dashi amma ya roketa da kada ta kuskura ta nuna ta sanshi don kada su kashe shi.

Ta ce yawancinsu sun koma da ciwuka da kumburarrun kafafu saboda sai da suka umarcesu da su bar takalmansu a makarantar kafin a sace su.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun bamu lambobin waya, sun ce za su zo neman aurenmu, 'Yammatan Jangebe

A wani labari na daban, ma'aikatan tallafi da ke taimakon 'yan gudun hijira a halin yanzu suna cikin wani hali bayan 'yan ta'adda sun kaddamar da hari a Dikwa.

Mayakan ta'addancin duk 'yan ISWAP ne, wani sashe na 'yan ta'adda da suka rabu da Boko Haram.

Harin yana zuwa ne bayan kwanaki kadan da shugaban rundunar sojin kasa ya kai ziyara babban sansanin sojin da ke yankin.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Online view pixel