Satar 'yan makaranta: Wasu jama'a ne ke yunkurin tozarta wannan gwamnatin, Sirika

Satar 'yan makaranta: Wasu jama'a ne ke yunkurin tozarta wannan gwamnatin, Sirika

- Ministan Buhari ya ce satar yaran makaranta duk yunkuri ne na tozarta gwamnati da wasu ke yi

- Ministan ya ce gwamnatin ta sha alwashin bai wa rayuka da dukiyoyin tsaro ballantana yaran makaranta

- Sirika ya ce babu shakka wannan satar yaran makarantar Jangebe na jihar Zamfara shine na karshe

Ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, ya ce akwai shirin cewa 'yan ta'adda za su iya sace wasu jama'an domin su tozarta gwamnatin tarayya.

Ministan ya sanar da hakan ne a ranar Litinin bayan ganawa da yayi da shugaban kasa Muuhammadu Buhari, The Cable ta wallafa.

Tun a farko ministan ya mika alkawarin shugaban kasa Muhammadu Buhari inda yace sace yaran makarantar sakandare na Jangebe zai zama na karshe a kasar nan.

Sirika ya ce akwai shirye-shirye da ake yi domin tabbatar da cewa an baiwa makarantu tsaro.

KU KARANTA: Sule Lamido: Salihu Yakasai ya fi Adesina da Garba Shehu jarumta

Satar 'yan makaranta: Wasu jama'ane ke yunkurin tozarta wannan gwamnatin, Sirika
Satar 'yan makaranta: Wasu jama'ane ke yunkurin tozarta wannan gwamnatin, Sirika. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

Ya ce gwamnatin tarayya ta na daukan dukkan matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron dukkan 'yan Najeriya ballantana yaran makaranta.

"Tabbas akwai yuwuwar wasu za su kara yi domin tozarta gwamnati,amma gwamnati tana da kayan aikin da za ta cigaba da tsare kasar," yace.

"Muna tunani kuma muna fata da izinin Allah wannan ne zai zama na karshe da za mu gani a kasar nan.

"Duk abinda zai yuwu kowacce irin gwamnati ta tsara domin tabbatar da tsaron rayuka da kadarori mun hada domin tabbatar da hakan bai sake faruwa ba. Kamar yadda nace, abu ne da ke faruwa kuma gwamnati ta mayar da hankali domin hakan."

KU KARANTA: Zan halarci mukabalar da aka shirya mana da malaman Kano, Sheikh Kabara

A wani labari na daban, a ranar Lahadi, mayakan ta'addanci na ISWAP sun kaiwa wani babban kwamandan sojojin Najeriya, Farouq Yahaya farmaki.

Farouq Yahaya, soja mai mukamin Manjo Janar, ya zama kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole a watan Afirilun 2020 bayan saukar Manjo Janar Olusegun Adeniyi.

HumAngle ta gano cewa mayakan ISWAP sun kai masa harin ne a kauyen garin Kuturu da ke tsakanin Auno da Jakana kusa da babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng