2023: Kwankwaso ya jinjinawa Wike, ya ce ya shirya zama 'shugaban ƙasa'

2023: Kwankwaso ya jinjinawa Wike, ya ce ya shirya zama 'shugaban ƙasa'

- Tsohon gwamnan jihar Kano ya ce gwamnan Rivers Nyesome Wike ya shirya zama shugaban ƙasa

- Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya yi a Rumuogba yayin kaddamar da gadar fly over a Rivers

- Wike a ɓangarensa ya yi wa jama'ar jiharsa alƙawarin sake gina wasu gadojin biyar kafin karewar wa'adinsa

Tsohon gwamnan Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bukaci gwamnan jihar Rivers, Nyesome Wike ya shirya yin aiki a 'matakin ƙasa' bayan kammala wa'adinsa a 2023, The Punch ta ruwaito.

Kwankwaso ya bayyana hakan ne bayan ƙaddamar da gadar flyover ta Rumuogba a ƙaramar hukumar Obio/Akpor a ranar Talata a jihar Rivers.

2023: Kwankwaso ya jinjinawa Wike, ya ce ya shirya zama 'shugabancin ƙasa'
2023: Kwankwaso ya jinjinawa Wike, ya ce ya shirya zama 'shugabancin ƙasa'. Hoto: @MobilePunch
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: 'Yan bindiga sun kashe yayan Sanata Suswam da hadiminsa a Benue

Tsohon gwamnan Kanon ya shaidawa Wike, "Mai girma gwamna, ka ci gaba, ka cigaba da yin abinda ya dace. Gwamna babban ƙallubale ne. Ba wasa bane.

"Kwangila ce tsakanin ka da jama'arka na shekaru takwas. Yanzu mun kusa kammala shekaru shida. Saura mana shekaru biyu a gidan gwamnati a nan jihar Rivers, bayan nan da izinin Allah za ka yi gaba zuwa aiki a 'matakin ƙasa'.

A jawabinsa, Wike yace, "A wuri na jihar Rivers ta cancanci morar abinda ya dace. Na fadawa mataimaki na da tawaga ta cewa duk da wa'adin mu na biyu ne wannan, za mu yi aiki kamar wa'adin farko muke. Abinda muke yi kenan."

KU KARANTA: An kuma: 'Yan bindiga sun sake garkuwa da fasinjoji 50 a Neja

Wike ya shaidawa mutanen jiharsa cewa nan da makonni biyu kamfanin Julius Berger Za ta dawo don rattaba hannu kan kwangilar gina cibiyar kansa da ciwon zuciya a jihar wanda babu irinsa a ƙasar kuma za a kammala cikin watanni 14.

Ya ce ƙaddamar da gadar ta Rumuogba ta bawa mutane da dama mamaki domin ba su taba zaton za a iya irin wannan aikin ba.

Ya yi wa jama'ar jihar albishir da wasu gadojin na flyover guda biyar cikin watanni 12 masu zuwa.

A wani labarin daban, kun ji Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi, NDLEA, ta kama wani mai fataucin miyagun kwayoyi mai shekaru 36 dauke da hodar Iblis da ta kai na Naira biliyan daya.

NDLEA ta ce mai safarar, Nkem Timothy, wanda ya yi basaja a matsayin Auwalu Audu domin yin fataucin kunshin hodar Iblis da nauyinsa ya kai 1.550kg. An yi kiyashin kudinsa ya kai Naira biliyan 1.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi ya ce an kama wanda ake zargin ne yayin da ya ke kokarin zuwa Algeria ta bodar jamhuriyar Nijar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: