NASRDA: Buhari ya yi sabon nadin mukami a Gwamnati, ya aikawa ‘Yan Majalisa sunan Shaba

NASRDA: Buhari ya yi sabon nadin mukami a Gwamnati, ya aikawa ‘Yan Majalisa sunan Shaba

- Buhari ya rubutawa Sanatoci takarda su tantance Halilu Shaba Ahmad

- Dr. Halilu Shaba Ahmad ne aka zaba ya jagoranci ma’aikatar NASRDA

- Ana so a tantance Ahmed a Majalisar dattawa ba tare da bata lokaci ba

Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattawa ta amince da nadin Dr. Halilu Shaba Ahmad a matsayin darektan hukumar NASRDA.

Punch ta ce Halilu Shaba Ahmad ne ake sa rai zai jagoranci aikin wannan hukuma da ke kula da nazari da binciken harkokin sama jannati ta Najeriya.

Jaridar ta rahoto cewa shugaban majalisar dattawa, Ahmad Ibrahim Lawan, ya karanto wasikar shugaban kasar a ranar Talata, 2 ga watan Maris, 2021.

Kamar yadda Sanata Ahmad Lawan ya bayyana, Mai girma Muhammadu Buhari ya roki ‘yan majalisa su yi maza-maza su tantance Shaba Ahmad.

KU KARANTA: Najeriya ta na da fetur da zai yi kwana 40 ana sha bai yanke ba - NNPC

Tun a tsakiyar 2020 Dr. Shaba Ahmad yake rike da kujerar NASRDA a matsayin shugaban rikon kwarya bayan wa’adin Farfesa Seidu Mohammed ya cika.

Kafin yanzu, Jonathan Angulu ya rike NASRDA domin sabon Darekta Janar din ya ji dadin karbar ragamar hukumar daga hannun tsohon shugaban hukumar.

Jonathan Angulu ya yi kwanaki biyu a ofis, sai ya mika wa Dr. Ahmad kujerar rikon kwaryar, kafin a nada sabon shugaba wanda zai kula da NARSDA ta kasa.

Kafin yanzu Shaba Ahmad ya rike kujeru da-dama a NASRDA, tun bayan zuwansa hukumar a 2009, Ahmad ya shafe shekaru fiye da 10 kenan a NARSDA.

KU KARANTA: Buhari ya jagoranci taron NSC da Hafsoshin Sojoji

NASRDA: Buhari ya yi sabon nadin mukami a Gwamnati, ya aikawa ‘Yan Majalisa sunan Shaba
Shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan
Asali: Facebook

Sabon shugaban ya rike darekta na dabaru a hukumar. Kafin zuwansa NARSDA, Ahmad ya kai matsayin mataimakin darekta a NEMA tsakanin 2006 da 2009.

Kwanaki kun ji cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada Manjo-Janar Samuel Adebayo a matsayin sabon babban hafsan leken asirin tsaro na Najeriya (CDI).

Janar Samuel Adebayo shi ne zai rike matsayin shugaban hukumar leken asirin tsaro na kasa.

Hakan na zuwa ne bayan shugaba Buhari ya sallami Janar Tukur Buratai, da sauran hafsosin tsaro, ya nada sabababi bayan sun shafe shekaru kusan shida a ofis.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Online view pixel