Gwamnatin Yobe ta rufe dukkanin makarantun kwana a fadin jihar

Gwamnatin Yobe ta rufe dukkanin makarantun kwana a fadin jihar

- Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya yi umurnin rufe dukka makarantun kwana a fadin jihar

- Sai dai ba a bayyana dalilin daukar wannan mataki ba amma ana ganin ba zai rasa nasaba da sace dalibai da aka yi a wasu jihohi ba

- An tattaro cewa tuni iyaye suka kwashe ‘ya’yansu dalibai da taimakon jami’an tsaro

Gwamnatin Jihar Yobe ta ba da umarnin rufe dukkan makarantun kwana a fadin kananan hukumomi 17 na jihar.

Duk da cewa jami’an jihar basu bayyana dalilin rufe makarantun ba, amma an fahimci cewa umurnin ba zai rasa nasaba da sace dalibai ba a jihohin Zamfara da Neja.

KU KARANTA KUMA: Ba da ni ba: Auren jinsi ba zai taba faruwa a muulkina ba, Shugaban kasar Ghana

Gwamnatin Yobe ta rufe dukkanin makarantun kwana a fadin jihar
Gwamnatin Yobe ta rufe dukkanin makarantun kwana a fadin jihar Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Wata majiya a daya daga cikin makarantun ta bayyana cewa umarnin rufe makarantun ya isa gare su da safiyar yau Lahadi, Daily Trust ta ruwaito.

A cewarsa, iyaye tare da taimakon jami'an tsaro sun zo da sassafe inda suka kwashe daliban Kwalejin 'Yan Matan Gwamnati da ke Damaturu.

Amma, ya ce umarnin ba zai shafi daliban SSS 3 ba.

Kwamishanan ilimin firamare da sakandare na jihar Dr Sani Idriss, bai samu damar yin tsokaci ba a lokacin da aka shigar da wannan rahoton saboda bai amsa kira ba balle ya amsa sakon tes da aka tura masa.

Jihohin Neja, Zamfara da Kano wasu jihohin ne da suka rufe makarantu kwanan nan.

A wani labarin, a baya mun kawo muku rahoton cewa, an saki daliban makaranta sakandaren 'yan mata dake Jangebe a jihar Zamfara. Sai dai,a yanzu mun samu rahoto daga tushe mai karfi cewa ba a sake su ba tukuna.

Daliban da aka sace daga makarantar sakandaren 'yan mata ta gwamnati, Jangebe, a karamar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara, har yanzu suna tare da wadanda suka sace su, in ji gwamnatin jihar.

KU KARANTA KUMA: Jam'iyyar APC ta lashe zaben kananan hukumomi 17 a jihar Yobe

Yusuf Idris, mai taimaka wa Gwamna Bello Matawalle a harkar yada labarai, ya shaida wa PremiumTimes da misalin karfe 3 na rana, a ranar Lahadi cewa har yanzu ana ci gaba da kokarin ganin an sake su.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel