Sule Lamido: Salihu Yakasai ya fi Adesina da Garba Shehu jarumta

Sule Lamido: Salihu Yakasai ya fi Adesina da Garba Shehu jarumta

- Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa ya ce Dawisu ya fi Adesina da Shehu jarumta

- An kama Salihu Yakasai a ranar Asabar bayan ya caccaki Buhari a kan matsalar tsaro

- Ya ce jinin gwagwarmayar siyasa a jinin Alhaji Tanko Yakasai yake da zuri'arsa

Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule lamido, ya ce Salihu Tanko Yakasai, tsohon hadimin Ganduje na jihar Kano, yafi Femi Adesina da Garba Shehu jarumta.

An kama Salihu a ranar Asabar bayan ya yi kira ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da yayi murabus sakamakon yawaitar rashin tsaro a kasar nan.

Labarin damke shi da aka yi ya karade gari yayin da Ganduje ya sanar da cewa ya sallame shi daga aiki, Daily Trust ta wallafa.

A yayin martani a wata takardar da Lamido ya fitar ranar Litinin, ya ce Salihu jarumi ne kamar mahaifinsa wanda ya tsaya tsayin daka kuma ya gagari miyagun shugabanni.

KU KARANTA: Hotunan katafaren gidan da hamshakin mawaki Don Jazzy ya tamfatsa

Sule Lamido: Salihu Yakasai ya fi Adesina da Garba Shehu jarumta
Sule Lamido: Salihu Yakasai ya fi Adesina da Garba Shehu jarumta. Hoto daga @daily_Trust
Asali: Twitter

"Ya dace gwamnati da jami'an tsaro su san abinda suke yi tare da kiyayewa wurin mu'amala da kananan fushi na matasa a kan siyasa. Ya dace a yi wasu bincike kadan a kan jinin Saliku Tanko kafin a fara sanin yadda za a yi da shi a kan kalamansa.

"Mahaifin Salihu, Alhaji Tanko Yakasai ya yi rayuwarsa ne yana magana a kan daidai tun daga lokacin turawan mulkin mallaka zuwa samun 'yancin kai zuwa mulkin soji da na farar hula.

"Alhaji Tanko Yakasai mai shige da fice daga wannan gidan yarin zuwa wani fiye da yadda zai iya tunawa. Abinda hakan ke nufi shine a jinin Tanko lamarin yake domin ya bi jini ne," yace.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan bindiga sun sako 'yan makarantar Kagara, amma akwai wasu kalubale

A wani labari na daban, hukumar tsaro ta fararen kaya (DSS) ta damke Salihu Tanko-Yakasai, mai magana da yawun gwamna Kano, Abdullahi Umar ganduje bayan ya ce gwamnatin APC ta gaza.

A ranar Juma'a, Tanko-Yakasai ya bayyana damuwarsa a kan labarin kwashe yara mata na makarantar sakandaren kwana da ke Jangebe a jihar Zamfara.

Bayan sa'o'i kadan da yin tsokacin a shafinsa a Twitter, an nemi Yakasai ko kasa ko sama an rasa, The Cable ta wallafa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel