Bidiyo: Garkuwa da 'yan makaranta da 'yan bindiga ke yi karamin laifi ne, Sheikh Gumi

Bidiyo: Garkuwa da 'yan makaranta da 'yan bindiga ke yi karamin laifi ne, Sheikh Gumi

- Sheikh Ahmad Gumi ya ce garkuwa da kananan yara da 'yan bindiga ke yi karamin laifi ne

- A cewar Malamin, gara satar yaran makaranta da kutse a kauyuka suna kashe jama'a

- Gumi wanda ya samu ganawa da 'yan bindiga a dajika, ya ce a yanzu suna daraja rayukan jama'a

Babban malamin addinin Islama kuma tsohon babban alkalin yankin arewa, Ahmad Gumi ya kwatanta garkuwa da yaran makaranta da 'yan bindiga ke yi da karamin laifi.

Gumi ya ce garkuwa da yaran makaranta da 'yan bindiga ke yi ba babban laifi bane idan aka hada shi shiga kauyuka tare da kashe jama'a da suke yi.

Gumi ya sanar da hakan ne yayin tattaunawa da bangaren Pidgin na BBC.

KU KARANTA: Zan halarci mukabalar da aka shirya mana da malaman Kano, Sheikh Kabara

Bidiyo: Satar 'yan makaranta karamin laifi ne, Sheikh Gumi
Bidiyo: Satar 'yan makaranta karamin laifi ne, Sheikh Gumi. Hoto daga @Thenation
Asali: Twitter

Malamin ya ce ganawarsa da 'yan bindiga ya haifar da da mai ido domin kuwa yanzu 'yan bindigan suna kiyaye rayukan jama'a.

Kamar yadda Gumi yace: "Garkuwa da yaran makaranta karamin laifi ne saboda daga karshe za a yi sasanci da iyayensu kuma yanzu 'yan bindiga suna kiyaye rayukan jama'a.

“Kafin nan, aikin 'yan bindigan shine zuwa garuruwa, kakkabe jama'a da kashe su. A yanzu haka zan iya cewa da'awa ta yi aiki kuma muna da burin kawo karshen 'yan bindigan Zamfara da sauran jihohi.

“'Yan bindiga yanzu suna kiyaye rayuka kuma harinsu kawai domin janyo magana ne."

KU KARANTA: Kagara: 'Yan bindiga basu tausayi ko tsoro, sun ce alkawarinsu gwamnati ta karya, Hauwa

A wani labari na daban, tsohon gwamnan jihar Osun kuma ministan cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbesola a ranakun karshen mako ya musanta labarin da ke yawo na cewa ya samu albashinsa na watanni 96 a sirrance a lokacin da yayi shugabancin jihar.

Ya kwatanta rahoton da labarin kanzon kurege wanda aka hada shi domin zubar da nagartar Ogbeni Rauf Aregbesola.

A wata takarda da hadimin Aregbesola na yada labarai, Soka Fasure ya fitar, ya ce rahoton da ake yaduwa a yanar gizo ya saba dokokin jaridanci, The Nation ta wallafa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel