'Sau 10 aka kama ni', Tanko Yakasai ya yi martani kan tsare ɗansa

'Sau 10 aka kama ni', Tanko Yakasai ya yi martani kan tsare ɗansa

- Alhaji Tanko Yakasai, mahaifin, Salihu Tanko Yakasai Ɗawisu ya ce ba yau hukuma ta fara kama iyalansa ba

- Ɗan siyasar na jamhuriya ta farko yana daga cikin waɗanda aka kama a 1983 bayan juyin mulkin da Buhari ya yi wa Shagari

- Tanko Yakasai da ya ce sau 10 aka kama shi a rayuwarsa don haka bai yi mamakin kama dansa da aka yi ba

- Yakasai ya ƙara da cewa babu wani laifi da ɗan sa ya yi illa sukar gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari

Tanko Yakasai, mahaifin korarren hadimin Gwamna Abdullahi Ganduje, Salihu Tanko Yakasai ya ce kama ƴan gidansu ba sabon abu bane, Daily Trust ta ruwaito.

Jami'an hukumar farar hula DSS, a ranar Juma'a sun kama Salihu Yakasai bayan ya soki gwamnatin Buhari kan rashin tsaro.

DUBA WANNAN: Mutum 9 sun mutu, 41 sun jikkata sakamakon hatsarin mota a Kano

'Sau 10 aka kama ni', Tanko Yakasai ya yi martani kan tsare ɗan sa
'Sau 10 aka kama ni', Tanko Yakasai ya yi martani kan tsare ɗan sa. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Yakasai, wanda ya yi hira da Daily Trust ta wayar tarho ya ce bai yi mamakin kama ɗan sa da aka yi ba.

Tanko Yakasai na daga cikin ƴan siyasa da gwamnatin Muhammadu Buhari ta mulkin soja ta tsare a 1983, bayan juyin mulkin da ta hamɓarar da gwamnatin Shehu Shagari.

KU KARANTA: Timothy ya yi basaja a matsayin Auwalu domin safarar hodar iblis ta N1bn ta bodar Sokoto

Yakasai na jami'in sadarwa, (PLO) na ofishin shugaban kasa a gwamnatin Shagari.

A sanarwar da ta fitar a ranar Asabar da yamma, DSS ta ce Yakasai yana hannunta amma an tsare shi ne kan wasu laifuka da ba su da alaka da "fadin ra'ayinsa a dandalin sada zumunta".

Amma mahaifinsa, Tanko Yakasai ya ce babu laifin da ɗansa ya yi illa sukar gwamnati.

Ɗan siyasar na jamhuriyar ta farko ya ce yana jira ya ga matakin da DSS za ta ɗauka zuwa ranar Litinin kafin ya san matakin da zai ɗauka.

A wani labarin daban, ofishin mai bawa Shugaban Kasa shawara kan Tsaro da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, a jiya sun sha banban kan kaddamar da fasahar sadarwa ta 5G a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Sun yi magana ne a Abuja yayin wani taro da kwamitocin Majalisar Dattawa kan Sadarwa, Kimiyya da Fasaha, da Yaki da Laifukan Yanar Gizo da Lafiya da Cututtuka masu Yaduwa suka shirya kan matsayin fasahar 5G.

A yayin da Pantami ya ce Najeriya ta shirya tsaf domin kaddamar da fasahar 5G, ofishin NSA ta nuna damuwarta kan wasu matsaloli da ke tattare da fasahar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe kimanin shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel