A karshe, Fani-Kayode ya watsawa Gwamna Bello kasa, yace ba zai bar PDP ya koma APC ba

A karshe, Fani-Kayode ya watsawa Gwamna Bello kasa, yace ba zai bar PDP ya koma APC ba

- Mr. Femi Fani-Kayode ya ce ya na nan a Jam’iyyar PDP, bai sauya-sheka ba

- Tsohon Ministan ya kawo karshen jita-jitar da ake ta yi cewa ya koma APC

- Fani-Kayode ya bayyana cewa an dinke barakar da aka samu da shi a PDP

Tsohon Ministan harkokin jiragen sama, Femi Fani-Kayode ya tsaida magana cewa ba zai sauya-sheka daga PDP ya koma wa jam’iyyar APC mai mulki ba.

Vanguard ta rahoto Femi Fani-Kayode ya na cewa barin jam’iyyar PDP bai cikin lissafi, kamar yadda wasu su ka yi ta rade-radin cewa zai bi tafiyar APC.

A cewar babban jigon na PDP, an shawo kan sabanin da ke tsakaninsa da jam’iyya. Fani-Kayode ya ce babban abin da ke gabansu shi ne hangen zaben 2023.

FFK kamar yadda ake yi masa lakabi, ya bayyana haka ne ranar Laraba bayan ya hadu da shugaban PDP, Prince Uche Secondus da wasu kusoshin NWC.

KU KARANTA: Fani-Kayode ya mani maganar shiga APC - Gwamna

Rahotanni sun ce Prince Uche Secondus ya jagoranci wasu ‘yan majalisar NWC sun kai wa tsohon Ministan ziyara har gidansa a babban birnin tarayya Abuja.

“Mun yi doguwar tattaunawa da ta kawo nasara, kuma ina son in yi magana a nan cewa duk matsalolin da aka samu, an shawo kansu.” Inji Fani-Kayode.

Ya ce: “Za mu cigaba da aiki tare, ban taba barin PDP ba, ina PDP, ina alfahari da zama na a nan,”

“Duk wata matsala da aka samu da abin da ke faru wa da kasar mu yanzu, abin da ya fi dace wa shi ne a zauna ba tare da la’akari da siyasa, addini, kabilanci ba.”

KU KARANTA: Dalilin da ya sa na gana da shugabannin APC - FFK

A karshe, Fani-Kayode ya watsawa Gwamna Bello kasa, yace ba zai bar PDP ya koma APC ba
Femi Fani-Kayode Hoto: legit.ng
Asali: UGC

Femi Fani-Kayode ya ji dadin yadda manyan jam’iyyarsa su ka ziyarce sa, kuma ya yaba da aikinsu, ya ce ba don jagorancin Uche Secondus ba, da PDP ta watse.

Kwanaki ne Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya fito ya na tabbatar da labarin da ya bi gari na cewa Femi Fani-Kayode, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.

Hakan na zuwa ne bayan babban jigon na jam’iyyar PDP a kudancin Najeriya ya gana da wasu kusoshin APC, daga ciki har da shugaban rikon kwarya, Mala Buni.

Bayan wannan magana, Fani-Kayode ya fito ya maida martani, ya ce bai yanke shawara ba tukuna.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng