Yanzu Yanzu: Jihar Katsina ta bada umarnin a sake bude makarantu

Yanzu Yanzu: Jihar Katsina ta bada umarnin a sake bude makarantu

- An umurci dukkan makarantun kwana a jihar Katsina da su sake budewa domin gudanar da harkokin karatun su

- Kwamishinan ilimi na jihar ne ya sanar da umarnin sake budewar

- Idan za a tuna wasu dalibai da aka sace a Kankara sun dawo jihar Katsina bayan kimanin mako guda da kwashe su

Wani rahoto da jaridar The Punch ta fitar ya nuna cewa an umurci makarantun kwana a jihar Katsina da su sake budewa a ranar Talata, 2 ga watan Maris.

Kwamishinan ilimi na jihar Badamosi Charanchi ne ya sanar da umarnin a ranar Lahadi, 28 ga watan Fabrairu.

Da yake karin haske game da umarnin bayan ganawarsa da manyan jami’ai a ma’aikatar sa, Charanchi ya ce daliban makarantun kwana na sojoji guda hudu da ke jihar za su koma karatu gadan-gadan.

Yanzu Yanzu: Jihar Katsina ta bada umarnin a sake bude makarantu
Yanzu Yanzu: Jihar Katsina ta bada umarnin a sake bude makarantu Hoto: @GovernorMasari
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Iyayen daliban Zamfara sun bayyana tsoron da suke ji a kan 'ya'yansu

Makarantun sun hada da ta sakandaren sojoji na gwamnati, Faskari; makarantar sakandaren sojoji na gwamnati ta Musawa; sakandaren sojoji na gwamnati ta 'yan Mata, Barkiya, da makarantar sakandaren' yan sanda, Mani.

Kwamishinan ya ci gaba da bayyana cewa ɗalibai maza a sauran makarantu su je makarantar sakandare mafi kusa da wuraren zamansu yayin da takwarorinsu mata za su jira jin mataki na gaba.

A gefe guda, Gwamnatin Jihar Yobe ta ba da umarnin rufe dukkan makarantun kwana a fadin kananan hukumomi 17 na jihar.

Duk da cewa jami’an jihar basu bayyana dalilin rufe makarantun ba, amma an fahimci cewa umurnin ba zai rasa nasaba da sace dalibai ba a jihohin Zamfara da Neja.

KU KARANTA KUMA: Yan bindiga sun kai hari garuruwa uku a Neja cikin sa’o’i biyu, sun kashe 3 da yin garkuwa da wasu da dama

Wata majiya a daya daga cikin makarantun ta bayyana cewa umarnin rufe makarantun ya isa gare su da safiyar yau Lahadi, Daily Trust ta ruwaito.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel