Ba da ni ba: Auren jinsi ba zai taba faruwa a muulkina ba, Shugaban kasar Ghana

Ba da ni ba: Auren jinsi ba zai taba faruwa a muulkina ba, Shugaban kasar Ghana

- Nana Akufo-Addo na kasar Ghana ya jadadda kyamarsa ga auren jinsi

- Shugaban kasar na Ghana ya ce ba za a taba yin wannan aure ba a karkashin shugabancinsa

- Ya bayyana matsayin nasa ne a ranar Asabar, 27 ga watan Fabrairu

Shugaban kasar Ghana, Nana Akufo-Addo, ya bayyana cewa auren jinsi ba zai taba faruwa ba a karkashin mulkin sa.

Ya fadi haka ne a wani taron coci da aka yi a Mampong ranar Asabar, 27 ga watan Fabrairu.

KU KARANTA KUMA: Jam'iyyar APC ta lashe zaben kananan hukumomi 17 a jihar Yobe

Ba da ni ba: Auren jinsi ba zai taba faruwa a muulkina ba, Shugaban kasar Ghana
Ba da ni ba: Auren jinsi ba zai taba faruwa a muulkina ba, Shugaban kasar Ghana Hoto: BBC.com
Asali: UGC

''Na fadi hakan a baya, kuma bari na sake jaddada cewa ba a karkashin Shugabancin Nana Akufo-Addo za a halatta auren jinsi a Ghana ba.

"Ba zai taba faruwa ba. Bari in maimaita; ba zai taba faruwa ba," in ji shi ga masu sauraro.

Bayanin nasa ya biyo bayan rufe wani ofishin LGBTQ + wanda aka bude kwanan nan a Accra, babban birnin kasar, jaridar Sahara Reporters ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Rana bata karya: Ganduje ya saka ranar mukabala tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman Kano

A wani labari na daban, kungiyar Dattawan Arewa (NEF) a jiya ta yi kira ga iyayen da ke da ’ya’ya a makarantun kwana a yankin arewa cewa kada su karaya game da yawan sace-sacen mutane ba kakkautawa a jihohin Zamfara da Neja, Daily Trust ta ruwaito.

Kungiyar, ta bakin Daraktan Yada Labarai da Bayar da Shawara, Dakta Hakeem Baba-Ahmed, ya kuma nuna kaduwa da haushi game da yawaitar sace-sacen yara ‘yan makarantar kwana a sassa daban-daban na Arewa.

Kungiyar, yayin kokawa game da karuwar hatsari ga rayuwar ‘yan Najeriya duk da tabbacin da gwamnatin tarayya ta bayar cewa za ta kawo karshen 'yan bindiga da sace-sacen mutane, ta bukaci iyaye da su bijire wa firgicin cire 'ya’yansu daga makarantu.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel