2023: Matasan Najeriya sun tara N10m don sayawa Tinubu tikitin takarar shugaban kasa

2023: Matasan Najeriya sun tara N10m don sayawa Tinubu tikitin takarar shugaban kasa

- Wasu matasa ‘yan Najeriya masu kaunar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu sun nuna sha'awarsu gareshi a zaben 2023

- Matasan Najeriya sun ce za su yi amfani da lokacin su wajen tabbatar da cewa Tinubu ya zama shugaban kasa a 2023

- Kungiyar matasan sun kuma tara kudi N10m ga Tinubu don siyan tikitin takarar shugaban kasa kafin 2023

Wata kungiyar matasa da aka fi sani da Tinubulate Nigeria Agenda (TINA) ta yi kira ga tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigo a jam’iyyar APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, da ya fito takarar shugaban kasa a zaben 2023 a karkashin inuwar jam’iyyar tasu mai mulki.

Don tabbatar da muhimmancin bukatarsu, kungiyar ta kuma tara zunzurutun kudi har Naira miliyan 10 don tallafawa Tinubu ya sayi tikitin takarar shugaban kasa.

Samuel Alamoh, babban daraktan kungiyar a wani taro wanda wakilin jaridar Legit.ng ya halarta a Abuja a ranar Juma'a, 26 ga watan Fabrairu ya bukaci Tinubu da ya shiga jerin 'yan takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

KU KARANTA: Jami'an tsaro sun fara sintirin ceton 'yan matan makarantar da aka sace a Zamfara

2023: Matasan Najeriya sun tara N10m don siyawa Tinubu tikitin takarar shugaban kasa
2023: Matasan Najeriya sun tara N10m don siyawa Tinubu tikitin takarar shugaban kasa Hoto: The Guardian
Source: UGC

Alamoh ya ce: “Kungiyar mu ta kammala shirye-shiryen gabatar da cekin kudi ga Tinubu domin sayan tikitin nuna ra’ayin tsayawa takarar shugaban kasa idan jam’iyya ta fara sayar da tikitin.

“Duk da cewa Asiwaju Tinubu yana da miliyoyin magoya baya da mabiya wadanda ko yaushe a shirye suke su taru don sayan tikitin takararsa, mambobinmu da magoya bayanmu da masu fatan alheri da kuma mabiya a duk fadin Najeriya sun yi imani da daukar nauyin a wuyansu.

"Wannan shine dalilin da ya sa muka hada 'yar karamar dukiyarmu don aiwatar da wannan kyakkyawan aiki matukar har tinubu ya bayyana a zahiri cewa yana sha'awar tsayawa matsayin dan takarar babbar jam'iyyar mu ta APC, a zaben shugaban kasa mai zuwa na 2023. ''

Alamoh ya bayyana TINA a matsayin rukuni na fitattun 'yan Najeriya masu mutunci kuma ƙwararru a fannoni daban-daban tare da ɗoki da jajircewa don nuna haɗin kai da soyayya da zaman lafiya a tsakanin 'yan Najeriya.

Ya ce mambobin kungiyar sun gamsu fiye da yadda ake tsammani cewa Tinubu yana da dukkan halaye, kwarewa, iyawa, kwazo da gogewa da ake bukata don tabbatar da ingancin Najeriya.

Ya kuma bayyana amincewar kungiyar ga Tinubu don jagorantar gwamnati tare da cikakkun manufofi wadanda suka hada da manyan kayayyakin more rayuwa da ci gaban dan adam tare da ci gaban tattalin arzikin da ba a taba gani ba.

Alamoh ya ce kungiyar na shirye-shiryen kaddamar da shiyyoyinta a dukkanin shiyyoyin siyasa shida na kasar nan kafin watan Maris 2021.

KU KARANTA: Majalisar Dattawa ta amince da N1.3bn don sayawa 'yan sanda barkonon tsohuwa

A wani labarin, Fastoci dauke da hotunan Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi na neman takarar shugaban kasa a shekarar 2023 sun bazu a jihar Adamawa.

Fastocin da aka fi gani a wasu muhimman wurare a Yola, babban birnin jihar Adamawa na dauke da rubutu da ke tallata Yahaya Bello a matsayin wanda ya dace ya zama shugaban kasar Nigeria.

Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.

Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.

A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.

Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez

Source: Legit.ng

Online view pixel