Yanzu nan: Boko Haram sun tare Matafiya a kan titin Damaturu-Maiduguri da rana tsaka

Yanzu nan: Boko Haram sun tare Matafiya a kan titin Damaturu-Maiduguri da rana tsaka

- ‘Yan ta’adda sun tare babban titin Damaturu zuwa Maiduguri yau da rana

- Ana zargin sojojin kungiyar Boko Haram ne su ka kai wannan sabon hari

- Sojojin kasa suna hanya domin ceto matafiyan da ‘yan ta’ddan suka dauke

Labarin da mu ke samu yanzu nan shi ne ‘yan ta’addan da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne, sun kai hari a kan hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

Rahotanni daga jaridar Yerwa Express sun bayyana cewa ‘yan ta’addan sun tare babban titin na jihar Borno, sun yi gaba da wasu matafiya da su ka samu.

Majiyar ta ce dakarun sojojin Najeriya sun samu labarin wannan hari, kuma sun yi maza sun maida martani, su na shirin ceto fasinjoji da aka yi gaba da su.

‘Yan ta’addan sun kai samame ne, su ka mamayi matafiyan domin gudun jawo hankalin wasu dakarun sojojin kasa wanda ba su da nisa da inda aka yi ta’adin.

KU KARANTA: Boko Haram sun yi garkuwa da fasinjoji 35 a hanyar Damaturu-Maiduguri

Wani matafiyi da ya tsira ya yi bayanin abin da ya faru, ya ce ‘yan ta’addan sun yi gab-da-gab da shi, amma ba su iya harbi ba saboda gudun a ji tashin bindiga.

“Na hange su, sai na yi maza na juya da sauri. Ko da cewa wata motarsu ta biyo, amma ba su iya kama ni ba.” Inji wannan matafiyi da ya sha da kyar a hanyar.

“Na tabbata abin da ya hana su harbi na shi ne ba su so sojojin da ba su da nisa da su, su lura da zuwansu.”

Kamar yadda jaridar ta bayyana, an tsare manyan motoci da-dama da fasinjoji a garin Jakana, yayin da sojoji su ke hanyar zuwa wannan wuri su tankare su.

Yanzu nan: Boko Haram sun tare Matafiya a kan titin Damaturu-Maiduguri da rana tsaka
Gwamna Babagaba Zulum Hoto: www.premiumtimesng.com
Source: UGC

KU KARANTA: An yi ba ta kashi tsakanin Sojoji da Boko Haram a Maiduguri

Inda aka kai wannan hari bai da nisa da garin Jakana, ana sa ran sojoji sun garzaya zuwa yankin.

Yayin da ake cigaba da kuka a kan matsalar rashin tsaro, mun ji cewa ‘Yan bindiga sun sheka da wasu samari zuwa barzahu a garin Sabuwa, da ke jihar Katsina.

Rahoton ya ce an kashe wasu samari uku, sannan an yi garkuwa da mata da-dama, daga ciki har da sabuwar aure a wannan hari da aka kai a ranar Talata da safe.

Wannan lamari ya auku ne ranar Talata, 23 ga watan Fubrairu, 2021, a wasu kauyuka uku: Mai Bakko, Kawarawa, da Unguwar Bako duk a cikin garin na Sabuwa

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel