Yanzu-yanzu: Dalibai da malaman Kagara da aka sako sun isa garin Minna

Yanzu-yanzu: Dalibai da malaman Kagara da aka sako sun isa garin Minna

- Dalibai da malaman kwalejin kimiyya ta Kagara sun isa garin Minna ta jihar Neja

- A safiyar yau ne aka tabbatar da sako daliban daga hannun 'yan bindigan da suka sace su

- Kwamishinan ilimi na jihar ne zai fara karbarsu kafin su samu ganawa da gwamnan

Dalibai tare da malaman kwalejin kimiyya ta Kagara da ke jihar Neja sun isa babban birnin jihar, Minna.

Dalibai 27, malamai 3 tare da wasu mutum 12 ne aka sace yayin harin da aka kai makarantar.

A wani bidiyo, an ga daliban suna fitowa daga dajin. An gano cewa an nadi bidiyon a wurin makarantar sakandare na Attahiru da ke Madaka a jihar Neja.

KU KARANTA: Sabon tashin hankali: 'Yan bindiga sun sheke mutum 22 a wurin hakar gwal a Zamfara

Yanzu-yanzu: Dalibai da malaman Kagara da aka sako sun isa garin Minna
Yanzu-yanzu: Dalibai da malaman Kagara da aka sako sun isa garin Minna. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Jibrin Usman, kakakin ma'aikatar ilimi ta jihar Neja ya ce an tuntubi kwamishinan ilimi na jihar domin ya karba yaran kafin su gana da gwamnan jihar.

Daya daga cikin iyayen daliban ya sanar da Daily Trust cewa an sako su kusa da Madaka a karamar hukuma Rafi ta Neja.

Mahaifin dalibin ya ce zai cire dan shi daga makarantar da gaggawa, inda ya kwatanta da hakan da abinda duk wani uba nagari zai yi.

KU KARANTA: Satar fasinjoji: Sojoji sun dakile Boko Haram a hanyar Damaturu zuwa Maiduguri

A wani labari na daban, wata babbar kotun jihar da ke zama a Owerri, babban birnin jihar Imo ta bada umarnin kwace dukkan kadarorin da ake zargin tsohon gwamna Rochas Okorocha ya mallaka ba ta halas ba yayin da yake kujerar gwamnan jihar daga 2011 zuwa 2019.

Mai shari'a Fred Njemanze ya bada umarnin bayan bukatar da babban lauyan Najeriya, Louis Alozie ya mika a madadin gwamnatin jihar, Channels TV ta ruwaito.

Wasu kadarorin da aka lissafa sun hada da jami'ar Eastern Palm da ke Ogboko, otal din Royal Spring Palm, kwatas din malaman IBC wacce aka ce gidauniyar Rochas ta samu ba bisa ka'ida ba, kwatas din majistare da sauransu.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng