Sabon tashin hankali: 'Yan bindiga sun sheke mutum 22 a wurin hakar gwal a Zamfara

Sabon tashin hankali: 'Yan bindiga sun sheke mutum 22 a wurin hakar gwal a Zamfara

- Wasu mutum 22 sun rasa rayukansu a Najeriya bayan 'yan ta'adda sun kai musu hari

- An halaka su ne a jihar Zamfara bayan 'yan bindiga sun bindige su a wurin hakar gwal

- Da farko mazauna sun hana 'yan bindigan shiga kauyensu amma daga bisani suka kutsa

A wani lamari mai taba zuciya a Najeriya, wasu 'yan bindiga sun bindige wasu mutane 22 a jihar Zamfara.

A ranar Alhamis, 25 ga watan Fabrairun 2021, 'yan bindiga sun kai samame inda suka kashe a kalla mtum 22, Daily Trust ta wallafa.

Kamar yadda aka gani, lamarin ya faru a wani wurin hakar zinari da ke kusa da Sabuwar Tunga a kauyen Dankurmi da ke karamar hukumar Maru.

KU KARANTA: Dalla-dalla: Yadda za a samu tallafin bashin FG ga masu kananan sana'o'i

Sabon tashin hankali: 'Yan bindiga sun sheke mutum 22 a wurin hakar gwal a Zamfara
Sabon tashin hankali: 'Yan bindiga sun sheke mutum 22 a wurin hakar gwal a Zamfara. Hoto daga DefenseInfong
Asali: Twitter

Kamar yadda wasu mazauna yankin suka sanar, 'yan bindigan sun kutsa wani kauyen na kusa mai suna Koda da niyyar satar shanu amma sai mazauna yankin suka bude musu wuta.

A takaice, an kashe shugaban 'yan bindigan a kauyen sannan suka kwace shanunsu da aka sace.

Bayan nan, sun shirya kansu inda suka tafi wurin hakar zinari da ke kauyen Sabuwar Tunga. Sun yi lambo yayin da mazauna kauyen suka je kasuwar mako a Dankurmi.

Kamar yadda majiyar tace: "Sun bukaci 'yan kasuwan da su zo taro amma lokacin da suka isa sai suka harbesu.

"Daga nan suka karasa wurin hakar zinari sannan suka dinga harbin jama'a bayan sun toshe dukkan hanyoyin tserewa."

KU KARANTA: Shekau ya magantu a kan tashin bama-bamai a Maiduguri da kwace gonarsa

A wani labari na daban, sojojin Najeriya sun datse farmakin da 'yan kungiyar ta'addanci ta ISWAP da Boko Haram suka kaiwa fasinjoji a kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu a Auno da ke jihar Borno.

Duk da sojin sun fatattaki 'yan ta'addan, majiyar sirri daga rundunar ta sanar da PRNigeria cewa an ceto fasinjoji masu tarin yawa da ke ababen hawa na haya a Auno.

Dakarun bataliya ta 212 da ke Jakana, Goni Masari da Auno sun gaggauta zuwa wurin sannan suka raka fasinjojin zuwa Damaturu da Maiduguri.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel