2023: Fastocin neman shugaban kasa na Gwamna Bello sun bazu a Adamawa

2023: Fastocin neman shugaban kasa na Gwamna Bello sun bazu a Adamawa

- Fastocin takarar shugaban kasa a 2023 na Gwamna Yahaya Bello sun bayyana a jihar Adamawa

- Kungiyar Nigeria Youth Awareness Group ce da dauki nauyin buga fastocin kamar yadda aka rubuta a jikinsu

- Wasu daga cikin mazaunin garin sun bayyana ra'ayoyinsu game da yiwuwar takarar da Yahaya Bello

Fastoci dauke da hotunan Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi na neman takarar shugaban kasa a shekarar 2023 sun bazu a jihar Adamawa.

Fastocin da aka fi gani a wasu muhimman wurare a Yola, babban birnin jihar Adamawa na dauke da rubutu da ke tallata Yahaya Bello a matsayin wanda ya dace ya zama shugaban kasar Nigeria.

2023: Fastocin neman shugaban kasa na Gwamna Bello sun bazu a Adamawa
2023: Fastocin neman shugaban kasa na Gwamna Bello sun bazu a Adamawa. @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Sheikh Ahmad Gumi ya yi martani kan sace ƴan matan makarantan Zamfara

Kamar yadda aka bayyana a jikin fastan, Kungiyar Nigeria Youth Awareness Group ce ta dauki nauyin fastocin da aka manna a wurare daban daban da suka hada da shatale-tale, allunan talla da wasu wuraren.

An gano fastocin da dama a wurare kan hanyar Numan zuwa Yola musamman bangaren titin da ke kusa da Filayen tashin jiragen sama na Yola da kuma mahadar PZ da ake kira shatale-talen Maidoki.

An kuma manna fastocin a bango da poll waya a shatale-talen Mubi, Mahadar Target da wasu muhimman wurare a birnin Yola.

Fastocin sun saka mutane sun bayyana ra'ayoyinsu kan yiwuwar neman takarar na Yahaya Bello.

KU KARANTA: FAAC: Jihohi 5 da suka samu kason kudi mafi tsoka a shekarar 2020

"Bari mu ga abinda zai yi idan ya zama shugaban kasa tunda shi matashi ne, " a cewar Abdullahi Usman, mazaunin Damilu, cikin garuruwan da aka manna fastocin na Yahaya Bello.

Wani Mustapha Raji, mazaunin State Low Cost ya ce wannan duk hayaniya ce irin ta yan siyasa.

"Ina ganin wannan mutumin (Yahaya Bello) yana yi wa wani sharan fage ne. Za mu ga yadda abubuwa za su kasance," in ji Mustapha Raji.

A kwananin baya an gano fastocin na Yahaya Bello a jihar Bauchi.

A wani labarin daban, ofishin mai bawa Shugaban Kasa shawara kan Tsaro da Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani, Isa Ali Pantami, a jiya sun sha banban kan kaddamar da fasahar sadarwa ta 5G a Najeriya, Daily Trust ta ruwaito.

Sun yi magana ne a Abuja yayin wani taro da kwamitocin Majalisar Dattawa kan Sadarwa, Kimiyya da Fasaha, da Yaki da Laifukan Yanar Gizo da Lafiya da Cututtuka masu Yaduwa suka shirya kan matsayin fasahar 5G.

A yayin da Pantami ya ce Najeriya ta shirya tsaf domin kaddamar da fasahar 5G, ofishin NSA ta nuna damuwarta kan wasu matsaloli da ke tattare da fasahar.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164