An ceto wata ma’aikaciyar gwamnati daga hannun masu garkuwa da mutane

An ceto wata ma’aikaciyar gwamnati daga hannun masu garkuwa da mutane

- Rundunar tsaro a jihar Bayelsa ta yi nasarar cafke wasu mutane biyu da ake zargi da garkuwa da mutane

- Maharan sun kama wata ma'aikaciyar gwamnati a bakin bindiga sannan suka tursasa ta cire kudi daga asusun bankinta ta hanyar amfani da ATM

- Hukumar yan sandan jihar ta tabbatar da lamarin inda ta sha alwashin yaki da laifuka a jihar

Tawagar tsaro na yan-sa-kai a jihar Bayelsa sun kama wasu masu garkuwa da mutane biyu da aka ce sun sace wata ma’aikaciyar gwamnati, Judith Adoga.

An tattaro cewa sun tsare Adoga da bindiga sannan suka tursasa ta zuwa wuraren cire kudi na ATM daban-daban inda suka cire wasu kudade daga asusun bankinta.

A yan baya-bayan nan a Yenagoa, babbar birnin jihar, miyagu kan tsare mutane da bindiga sannan su tursasa masu cire kudade daga ATM, Channels TV ta ruwaito.

An ceto wata ma’aikaciyar gwamnati daga hannun masu garkuwa da mutane
An ceto wata ma’aikaciyar gwamnati daga hannun masu garkuwa da mutane Hoto: @PremiumTimesng
Asali: UGC

KU KARANTA KUMA: Satar yan matan Zamfara: ‘Yan jarida tsun tsallake rijiya da baya

Miyagun sun kama matar ne a hanyar Imgbi a ranar 25 ga watan Fabrairu sannan suka tafi yawon neman POS don cire kudi lokacin da tawagar yan sandan SWAT suka far masu inda suka kama mutum biyu da ake zargi, Headman Eniyi da Ebi Tonbofa.

Abubuwan da aka kwato daga wajensu sun hada da bindiga da harsasai uku.

Rundunar yan sandan jihar Bayelsa ta tabbatar da lamarin a wani jawabin manema labarai da kakakinta, Asinim Butswat yayi.

“Za ku tuna cewa kwamishinan yan sanda, reshen jihar Bayelsa, CP Mike Okoli, ya umurci jami’an yan sanda da su tsamo yan fashi a lokacin da aka kai rahoto makamancin wannan hukumar yan sandan,” in ji shi.

“Bayelsa ta kasance daya daga cikin jihohi mafi tsaro ta fannin kasuwanci da zamantakewar mutane, don haka zai ci gaba da yin iya bakin kokarinsa wajen yaki da laifuka da ta’addanci kamar yadda ya rataya a wuyansa.”

Kamun da yan-sa-kai na jihar suka yi zai karfafa gwiwar mazauna jihar kuma zai sabonta fatan gwamnan jihar, Sanata Douye Diri, wanda a lokuta daban-daban ya bayyana cewa ba zai sa siyasa a tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a ba.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan mata 317 aka sace daga makarantar GGSS a Zamfara, yan sanda

A halin da ake ciki, an mika masu laifin ga rundunar SWAT don ci gaba da bincike da hukunta su.

A cewar hukumomin yan sandan, masu laifin na bayar da hadin kai a binciken da ake kuma za a mika su kotu da zaran an kammala bincike.

A wani labarin, jami'an tsaro da wata kungiyar tsaro ta sa kai sun fara neman 'yan mata sama da 400 da 'yan bindiga suka sace a safiyar ranar Juma'a daga makarantar su da ke Jengebe, jihar Zamfara, Arewa maso Yammacin Najeriya.

An sace 'yan matan makarantar ne lokacin da 'yan bindigan suka afkawa makarantar sakandaren 'yan mata ta gwamnati ta Jangebe sannan daga baya suka yi awn gaba da daliban.

Majiyoyi da yawa sun shaida wa walikin HumAngle cewa adadin 'yan matan makarantar da aka sace zai iya haura 417 yayin da wasu suka ce adadin na iya fin haka.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel