An sha dirama yayinda yan sanda da DSS suka yi yunkurin kama mai fafutukar Yarbawa, Sunday Igboho

An sha dirama yayinda yan sanda da DSS suka yi yunkurin kama mai fafutukar Yarbawa, Sunday Igboho

- An dakile wani yunkurin kama jigon matasan Yarabawa, Sunday Igboho, a ranar Juma’a, 26 ga watan Fabrairu

- Hadaddiyar tawagar ‘yan sanda da DSS sun tsare dan gwagwarmayar Yarbawan kan babbar hanyar Legas zuwa Ibadan a cewar tsohon minista Femi Fani-Kayode

- Igboho ya zama gwarzon dan kungiyar asiri bayan ya baiwa Fulani makiyaya wa’adin barin yankin Igangan na jihar Oyo

An shiga halin fargaba a garin Ibadan a ranar Juma’a 26 ga watan Fabrairu, lokacin da jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya da kuma jami’an tsaron farin kaya (DSS) suka yi yunkurin cafke Sunday Adeyemo, wani dan gwagwarmaya Yarbawa kuma shugaban matasa, Sunday Igboho.

A cikin bidiyon da tsohon ministan jirgin sama, Femi Fani-Kayode ya wallafa, jami'an tsaron sun tsayar da Igboho tare da yaran sa a babbar hanyar Legas zuwa Ibadan.

KU KARANTA KUMA: An ceto wata ma’aikaciyar gwamnati daga hannun masu garkuwa da mutane

An tattaro cewa dan fafutukan Yarbawan na kan "hanyarsa ta ganin Baba Ayo Adebanjo", wani dattijo yarbawa kuma daya daga cikin shugabannin Afenifere a Legas.

An sha dirama yayinda yan sanda da DSS suka yi yunkurin kama mai fafutukar Yarbawa,Sunday Igboho
An sha dirama yayinda yan sanda da DSS suka yi yunkurin kama mai fafutukar Yarbawa,Sunday Igboho Hoto: @OoduaFocus
Asali: Twitter

Fani-Kayode, wanda ya tabbatar da arangamar, ya ce ya yi magana da Igboho yayin da ya bayyana yunkurin kame shugaban matasan Yarbawan a matsayin "ganganci da hatsari."

"Na yi Allah wadai da wannan yunƙuri na kwanton bauna da sace shi. Ba wai sakaci ba ne kawai amma kuma yana da haɗari sosai. Idan jami'an tsaro suna son ganin shi duk abin da ya kamata su yi shi ne su gayyace shi zuwa ofishinsu. Ban san wani laifi da ya aikata ba kuma ina kira ga a kiyaye a dukkan bangarorin."

KU KARANTA KUMA: Satar yan matan Zamfara: ‘Yan jarida tsun tsallake rijiya da baya

A wani labari na daban, jami'an tsaro da wata kungiyar tsaro ta sa kai sun fara neman 'yan mata sama da 400 da 'yan bindiga suka sace a safiyar ranar Juma'a daga makarantar su da ke Jengebe, jihar Zamfara, Arewa maso Yammacin Najeriya.

An sace 'yan matan makarantar ne lokacin da 'yan bindigan suka afkawa makarantar sakandaren 'yan mata ta gwamnati ta Jangebe sannan daga baya suka yi awn gaba da daliban.

Majiyoyi da yawa sun shaida wa walikin HumAngle cewa adadin 'yan matan makarantar da aka sace zai iya haura 417 yayin da wasu suka ce adadin na iya fin haka.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel