Zan dafa wa mijina abinci sau uku a rana, wata budurwa ta sanar da mata masu tsatsauran ra’ayi
- Wata budurwa ta je shafin soshiyal midiya don bayyana yadda za ta dauke dawainiyar mijinta a gidan aurenta
- A bisa ga wallafarta, ta bayyana cewa za ta girkawa mijinta abinci sau uku a rana sai dai idan shi yace ta huta
- Wallafar tata ta haddasa cece-kuce a tsakanin masu amfani da shafin zumunta
Wata yar Najeriya mai amfani da shafin Twitter @xarah_bint ta haddasa cece-kuce a shafin soshiyal midiya bayan ta bayyana kudirinta na daukar dawainiyar mijinta.
A wani wallafa da ta yi kai tsaye zuwa ga mata masu tsatsauran ra’ayi kan maza, ta bayyana cewa za ta dunga girkawa mijinta abinci sau uku a rana.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gwamnatin Zamfara ta tabbatar da sace dalibai mata da yan bindiga suka yi
A kalamanta:
“Na zo nan domin na tunatar da wadannan yan mata masu tsatsauran ra’ayi cewa zan dunga girkawa mijina abinci sau uku a kulla-yaumin har sai dai idan shi ya zabi ya bari na huta.”
Kalli wallafarta a kasa:
Kalli sharhin masu amfani da shafin soshiyal midiya a kasa:
theaprokoroom:
“Har sai dai idan shi ya zabi ki huta? Ina fatan zai maki kamar yadda kike yi mai.”
callmemjay:
“Kina iya mayar da shi sau 4 a rana.”
priscaberry_perfumes:
“Ina taya ki murna uwar-girki! Zabinki ne, babu ruwanmu a ciki♂️♀️♀️"
tdemuren:
“Yanzu ki je ki karbi lambar yabonki...sannu da kokari!”
KU KARANTA KUMA: Dalla-dalla: Yadda za a samu tallafin bashin FG ga masu kananan sana'o'i
gracemaryenenche:
“Girka, kina iya girkawa makwantankin ma.”
mercy__silvanus:
“Zabinki ♀️. Duk da yadda na kai da son girki, ba zan girkawa kaina abinci sau 3 a rana ba.”
A wani labarin, gwamnan Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, a ranar Alhamis ya kai ziyara garin Dikwa inda ya rabawa al'ummar garin 34,000 kayan masarufi da kansa.
Mai magana da yawunsa, Malam Isa Gusau, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Alhamis, 25 ga Febrairu, 2021.
A cewarsa, gwamnan ya raba kayan masarufi daban-daban ga iyalai 34,00.
Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.
Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.
Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.
Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411
Asali: Legit.ng