Sheikh Ahmad Gumi ya yi martani kan sace ƴan matan makarantan Zamfara

Sheikh Ahmad Gumi ya yi martani kan sace ƴan matan makarantan Zamfara

- Sheikh Ahmad Gumi ya tuntubi yan bindgan Zamfara game da sace yan mata a GSS Jangebe

- Babban malamin ya ce yan bindigan da ya tuntuba sun ce masa ba su bane suka sace yan matan

- Shaihin malamin ya kuma ce akwai yiwuwar zai iya zuwa jihar ta Zamfara don ganin an sako matan

Malamin addinin musulunci Sheikh Ahmad Gumi ya ce ba yan bindigan da ya gana da su a dajin Zamfara bane suka sace yan matan makaranta a jihar.

The Nation ta ruwaito cewa yan bindigan sun afka makarantan Gwamnati na Jangebe a karamar hukumar Talata Mafara misalin karfe daya na daren Alhamis inda suka sace dalibai mata fiye da 300.

Sheikh Ahmad Gumi ya yi martani kan sace yan matan makarantan Zamfara
Sheikh Ahmad Gumi ya yi martani kan sace yan matan makarantan Zamfara. Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: FAAC: Jihohi 5 da suka samu kason kudi mafi tsoka a shekarar 2020

Kwamishinan tsaro da harkokin gida na Zamfara, Alhaji Abubakar Dauran ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai, NAN, sace yan matan amma bai tabbatar da adadin wadanda aka sace din ba.

Gumi, cikin gajeren hirar wayar tarho da jaridar The Nation, ya ce wasu kungiyar daban ne suka sace yan matan a Zamfara amma ba wanda ya gana da su ba.

Malamin addinin musuluncin wanda ya gana shugabanin yan bindigan a Zamfara ya ce ya tuntube su kuma sun ce, "Ba su ne suka sace yan matan makarantar ba, wata kungiyar ne daban."

Da aka masa tambaya ko zai tafi Zamfara domin ganawa da yan bindigan don a sako yan matan, Sheikh Gumi ya amsa da cewa, "wata kila".

KU KARANTA: Pantami da NSA sun sha banban kan batun ƙaddamar da fasahar 5G a Nigeria

Malamin ya tafi dazukan Zamfara domin yi wa yan bindigan nasiha sannan ya yi ji kokensu inda ya yi kira ga gwamnati ta duba yiwuwar yi musu afuwa.

Gumi da tawagarsa sun kuma gana da wasu yan bindigan a dazukan Sububu da Pakai.

A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel