Ba zan taba baiwa masu kiran Fulani da 'yan ta'adda hakuri ba, Gwamnan Bauchi
- Gwamnan Bauchi, sanata Bala Mohammed ya ce ba zai ba wa kowa hakuri ba akan fadin gaskiya da yayi
- Kamar yadda ya sanar a wani taro, babu wata kabila da za ta ce bata da masu aikata laifi a cikinta
- Ya ce yi wa kabila daya lakabi da zama 'yan ta'adda ko makasa na iya janyo rabuwar kai a kasar nan
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce ba zai taba bada hakuri ba a kan tsokacin da yayi a makon da ya gabata ga wadanda ke kwatanta 'yan kabilar Fulani da makasa ko masu garkuwa da mutane.
Idan za a tuna, gwamnan ya fuskanci manyan kalubale tare da caccaka bayan da yace makiyaya na da damar yawo da bindiga kirar AK-47 domin baiwa kansu kariya.
Mohammed wanda yayi jawabi a ranar Laraba yayin kaddamar da kamfen din yi wa dabbobi riga-kafi na 2020/2021 wanda aka yi a Galambi da ke jihar Bauchi.
KU KARANTA: Da duminsa: FG za ta fara shari'a da mutum 5,000 da ake zargi da ta'addancin Boko Haram
Ya ce yi wa kabila daya lakabi da miyagu bai dace ba kuma zai iya haifar da rashin hadin kai a kasar nan, The Nation ta wallafa.
Ya ce, "Mun kalubalanci yi wa Fulani lakabi da makasa ko masu garkuwa da mutane da ake yi. Ba zan taba bada hakuri ba saboda na fadi gaskiya kuma babu wata kabila da za ta ce babu masu laifi a cikinta."
KU KARANTA: Hotunan kyakyawar likita da jama'a ke cewa kyanta da murmushinta za su iya warkarwa
A wani labari na daban, dakarun sojin Najeriya sun samu nasarar kwato garin Marte daga hannun miyagun 'yan ta'addan Boko Haram, kakakin rundunar sojin kasa ya tabbatar da wannan cigaban.
Rundunar ta samu wannan nasarar ne a ranar Talata bayan umarnin da shugaban rundunar sojin kasa, Manjo Janar Attahiru ya basu tare da wa'adi.
Mohammed Yerima, kakakin rundunar ya tabbatar da wannan cigaban ga jaridar The Cable a ranar Talata. "Tabbas, mun sake kwace yankin," yace.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng