Ka zo mu tattauna, baka son kawo zaman lafiya, 'Yan bindiga sun gayyaci Buhari

Ka zo mu tattauna, baka son kawo zaman lafiya, 'Yan bindiga sun gayyaci Buhari

- 'Yan bindiga sun bukaci Buhari da ya je su tattauna tare da yin sasanci idan ana son zaman lafiya

- Kamar yadda aka zanta da daya daga cikinsu, ya ce a lokacin kamfen, Buhari ya zagaya kasar nan baki daya

- Ya zargi gwamnatin Buhari da nuna halin ko in kula ga rasa rayukan da ake yi tare da karya alkawarin da tayi tun farko

A cikin watannin nan, 'yan bindiga suna cigaba da cin karensu babu babbaka a arewacin kasar nan inda suke kai hari tare da yin garkuwa da mutane, The Cable ta wallafa.

Ahmad Gumi, fitaccen malamin addinin Islama ya samu ganawa da wasu 'yan bindigan a dajikan Zamfara inda ya bukaci su ajiye makamansu.

Sai dai a wata tattaunawa da Daily Trust, wani dan bindiga da ya rufe fuskarsa ya ce idan Buhari zai iya zagaya kasar nan dan yakin neman zabe, babu abinda zai hana shi zuwa su tattauna a kan zaman lafiya.

KU KARANTA: Kagara: Dogo-Gide, shugaban 'yan bindiga ya tuntubi iyayen yara a kan kudin fansa

Ka zo mu tattauna, baka son kawo zaman lafiya, 'Yan bindiga sun gayyaci Buhari
Ka zo mu tattauna, baka son kawo zaman lafiya, 'Yan bindiga sun gayyaci Buhari. Hoto daga @Thecableng
Asali: Twitter

Ya ce tun farko an sasanta da kungiyarsa amma babu dadewa aka bar su a daji ba tare da jin wani labari ba,

"Mun sasanta amma kuka bar mu a daji da bindigogi kuma babu sako ko dan aike. Me kuke tsammani? Ya kuke son mutum ya rayu? Duk alkawarurrukan da kuka yi mana baku cika ko daya ba," yace.

“Shugaban kasan da kan shi ya zo mu tattauna. Lokacin da yake kamfen ai ya iya zuwa ko ina, me yasa ba zai iya zuwa yanzu ba? Kullum kashe mutane ake yi saboda bai dauka sasancin da muhimmanci ba.

"Babu ranar da ke fitowa ta fadi ba a kashe mutum a Zamfara, Neja, Kaduna ko Katsina ba. Muna yabon Jonathan da Yaradua saboda Buhari ya kasa yin komai. Mun zabe shi ne saboda ya kawo gyara amma ya kasa."

KU KARANTA: Hotunan kyakyawar likita da jama'a ke cewa kyanta da murmushinta za su iya warkarwa

A wani labari na daban, gwamnatin tarayya ta ce nan babu dadewa za ta fara shari'ar wasu mutum 5,000 da ake zargi da zama 'yan ta'addan Boko Haram kuma suna tsare a gidajen gyaran halin kasar nan.

Darakta janar na kungiyar shari'a, Aliyu Abubakar, ya bayyana hakan a wata ziyara da ya kaiwa gwamnan Borno, Babagana Zulum a gidan gwamnati da ke Maiduguri.

Abubakar ya bayyana barikin Giwa da ke Maiduguri, gidan gyaran hali na Kainji a matsayin wuraren da aka adana wadanda ake zargin da ta'addanci, Daily Trust ta ruwaito.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng