Cikin Hotuna: Sabon shugaban hukumar EFCC ya kawai shugaba Muhammadu Buhari ziyara

Cikin Hotuna: Sabon shugaban hukumar EFCC ya kawai shugaba Muhammadu Buhari ziyara

- Kwana daya bayan tabbatar da shi, Bawa ya garzaya wajen Buhari

- Bawa na cikin daliban karon farko da aka diba a kwalejin hukumar EFCC

- Shine mutum mafi karancin shekaru da ya taba rike mukamin shugaban EFCC

Shugaba Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin sabon shugaban hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC, AbdulRashid Bawa.

Bawa ya ziyarci Buhari ne a fadar shugaban kasa dake birnin tarayya, Abuja ranar Alhamis, 25 ga watan Febrairu, 2021.

Ziyararsa ya biyo bayan tabbatar da shi da majalisar dattawan tarayya tayi ranar Laraba.

Majalisar dattawan Najerita ta amince da AbdulRasheed Bawa a matsayin sabon shugaban hukumar EFCC.

Shugaban majalisa, Sanata Ahmad Lawan, ya sanar da hakan a zauren majalisan ranar Laraba, 24 ga Febrairu, 2021.

Wannan ya biyo bayan tambayoyi da ya amsa yayinda ya gurfana gaban yan majalisan.

KU KARANTA: EFCC: Abubuwa 8 da Abdulrasheed Bawa ya fada da ya bayyana a zauren Majalisa yau

Cikin Hotuna: Sabon shugaban hukumar EFCC ya kawai shugaba Muhammadu Buhari ziyara
Cikin Hotuna: Sabon shugaban hukumar EFCC ya kawai shugaba Muhammadu Buhari ziyara Credit: @Buharisallau1
Source: Twitter

Abdulrasheed Bawa, ya yi magana a kan alakarsa da Ibrahim Magu.

Ya ce akwai dangantaka ta mutunci tsakaninsa da tsohon mukaddashin shugaban EFCC, Ibrahim Magu.

Da yake jawabi yau, Abdulrasheed Bawa ya bayyana yadda Magu ya kira shi a waya, ya taya shi murna a lokacin da aka zabe shi a matsayin sabon shugaban hukumar.

“Ina da alaka mai kyau da tsohon mukaddashin shugaban hukumar EFCC. Ya kira ni da aka zabe ni, ya yi mani fatan Ubangiji ya ba ni sa’a.” inji Abdulrasheed Bawa.

KU DUBA: Abubuwa 10 da ya kamata ka sani game da ‘Dan shekara 40 da zai jagoranci EFCC

Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin uku yanzu tare da shararriyar jarida Legit.

Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss.

Source: Legit.ng

Online view pixel