Tarzomar Billiri: Gwamnan Gombe ya yi alƙawarin tabbatar da zaman Lafiya.
-Jinkiri wajen naɗa babban sarkin ƙabilar Tangale ya haifar da tarzoma
-Wannan ne abin da ya haifar da ɗar-ɗar a zukatan waɗanda ba ƴan asalin jihar ba
-Saidai kuma gwamnan Gombe ya yi alƙawarin tabbatar da zaman lafiya a jihar
Jaridar The Tribune ta rawaito an dai ba da tabbacin ne ga baƙi waɗanda ba ƴan asalin jihar ta Gombe ba waɗanda kuma tarzomar garin Billiri ta shafa, inda gwamnati ta tabbatar musu da ƙoƙarinta wajen kare dukiyyi da rayukannsu.
An buƙaci mazauna wannan yanki da su koma wuraren kasuwancinsu ba tare da wata fargaba ta cin zarafi ko firgitarwa ba, matuƙar dai sun cigaba da kasancewa masu bin doka da oda.
Wannan tabbaci dai na zuwa ne daga bakin gwamnan jihar, Muhammadu Inuwa Yahaya, a yayin zaman sasantawa da shuwagabannin unguwannin bayan samun tarzomar da ta ɓarke a yayin zanga-zangar lumanar da matasa suka yi a ƙaramar hukumar Billiri a satin da ya gabata.
KARANTA WANNAN: Rikicin makiyaya gwamnan jihar bauchi ya roki fulani ka da su dauki AK-47
Masu zanga-zangar dai na yi ne saboda nuƙusani da ake yi wajen sanar da babban sabon sarkin Tangale ta ƙaramar hukumar Billiri.
Gwamna Yahaya ya cigaba da tabbatar da cewa zai yi komai wajen tabbatar da kowa dake Gombe na zaune lafiya ba tare da wani tsoro ba kamar yadda yake a Kundin Mulkin ƙasar nan na 1999 da a kai kwaskwarima.
A cewar gwamnan, babu wata dama da ta ba shi ikon cuzguna wa ƴancin wani, tunda yake dai ya yi ransuwa da kare al'umma ba tare da nuna son-kai na dagantaka ta addini da siyasa ba.
Gwamnan ya yi alla wadai da tarzomar kuma yana ganin baiken al'umma na gaza haƙuri domin ya sauke nauyin da mulki wajen zaɓen shugaban a matsayinsa na gwamna.
Ya cigaba da cewa shi bai saɓa wa wata doka ba tun daga sanda abin ya fara zuwa lokacin da zanga-zangar ta sauya zani da haifar da sanya dokar zaman kulle.
KARANTA WANNAN: Zargin taaddanci gwamnan Bauchi ya Ƙallubalanci Ortom.
Gwamnan ya ce, "Zan nuna ba-sani-ba-sabo ga duk wani nau'i na ta-da-zaune-tsaye. Zaman lafiya abu ne mai muhimmanci a gare mu kuma za mu yi duk abin da ya dace wajen tabbatar ba samu ɗaukar fansa ba."
A yayin amsa tambayoyi, babban mai ba wa gwamnan shawara kan Zamantakewa Tsakanin Al'umma, Chief Cornelius Ewuzie, ya yaba wa gwamnan wajen samar da zaman lafiya tare da tabbatar masa da goyon bayansa kan wannan nufi nasa.
Shuwagabannin yankuna daban-daban na baƙi mazauna Gombe sun nuna goyon baya da kuma ƙarfafa wa gwamnan a wannan yunƙuri nasa na tabbatar da zaman lafiya.
A wani labarin daban, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya roki Fulani makiyaya da kada su dauki bindiga AK-47 kuma su kasance cikin lumana.
Gwamnan, ya yi wannan rokon a jawabinsa a wajen kaddamar da allurar rigakafin dabbobi na shekara-shekara ta 2020/2021 da aka gudanar a Galambi Cattle Ranch da ke Bauchi, ranar Laraba, ya bayyana Fulani a matsayin masu tawali’u, masu sauƙin kai, da kawaici.
Ya ce, “Abin da zan yi, ba zan faɗi shi a nan ba, amma zan yi duk mai yiwuwa don tabbatar da na kare ku da kuma ba ku goyon baya saboda na san kuna da kyau.
Asali: Legit.ng