Yanzu-yanzu: COVID-19 ta yi ajalin Rear Admiral Aikhomu

Yanzu-yanzu: COVID-19 ta yi ajalin Rear Admiral Aikhomu

- Allah ya yi wa Rear Admiral Joe Aikhomu (mai murabus) ya rasuwa

- Admiral Joe Aikhomu ya rasu ne a yau Alhamis sakamakon cutar corona

- Aikhoma mamba ne na kwamitin bincike kan siyo makamai daga 2007 zuwa 2015 wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa a lokacin mulkinsa na farko

Tsohon shugaban sashin mulki na rundunar sojojin ruwan Nigeria, Rear Admiral Joe Aikhomu (mai murabus) ya rasu kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Aikhomu, mai shekaru 65, ya rasu ne a safiyar ranar Alhamis sakamakon annobar cutar coronavirus.

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Ɓata-gari sun kai wa 'yan sanda hari, sun kashe biyu, sun cinnawa motarsu wuta

Yanzu-yanzu: COVID-19 ta yi ajalin Rear Admiral Aikhomu
Yanzu-yanzu: COVID-19 ta yi ajalin Rear Admiral Aikhomu
Asali: Twitter

Marigayin, wanda kani ne ga tsohon mataimakin shugaban kasa, Admiral Augustus Aikhomu (mai murabus), kafin rasuwarsa, shine shugaban kamfanin Ocean Marine Solutions (OMS) wadda dan uwansa marigayi Kyaftin Hosa Okunbo ya kafa.

KU KARANTA: Abin da yasa muka tuba muka miƙa makamanmu, tsaffin 'yan bindigan Zamfara

Aikhoma mamba ne na kwamitin bincike kan siyo makamai daga shekarar 2007 zuwa 2015 wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya kafa a lokacin mulkinsa na farko.

A cewar majiyoyi, rasuwarsa ya girgiza rundunar sojojin ruwa duba da cewa kwararre ne kan ayyukan ruwa da zirga-zirga a yankin Guinea.

A wani labarin daban, basarake mai sanda mai daraja ta daya, Olupo na Ajase-Ipo, Oba Sikiru Atanda Woleola ya riga mu gidan gaskiya, The Nation ta ruwaito.

Marigayin sarkin, ya rasu ne misalin karfe 10 na daren ranar Lahadi, 21 ga watan Fabrairun 2021 bayan fama da gajeruwar rashin lafiya a garinsa da ke Ajase-Ipo kamar yadda aka ruwaito.

Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq na jihar Kwara ya yi wa masarautar da jama'ar karamar hukumar Ajase-Ipo ta'aziyya bisa rasuwar basaraken.

Aminu Ibrahim ɗan jarida ne kuma ɗalibi mai neman ilimi. Ya yi karatun digiri na farko a Jami'ar Ahmadu Bello Zaria, yanzu yana karatun digiri na biyu a Jami'ar Gwamnatin Tarayya da ke Dutse, Jihar Jigawa.

Ya shafe tsawon shekaru 5 yana aikin jarida inda ya samu gogewa a ɓangaren rubutun Hausa akan fanoni da suka shafi siyasa, mulki, wasanni, nishadi, da sauransu.

Aminu Ibrahim ne ya samu lambar yabo na zakaran editan shekarar 2020.

Za'a iya bibiyarsa a shafinsa na Twitter a @ameeynu

Asali: Legit.ng

Online view pixel