Hotuna da bidiyon yadda aka daga gida kacokan daga wata unguwa zuwa wata a Amurka

Hotuna da bidiyon yadda aka daga gida kacokan daga wata unguwa zuwa wata a Amurka

- An dauka wani gida kacokan a kasar Amurka inda aka sauya masa unguwa, mai gidan ya biya N152,300,000 don daukar gidan

- Gidan mai shekaru 139 yana San Francisco ne kuma an dauke shi kacokan inda aka sauya masa wuri

- Jama'a da dama mazauna yankin sun fito suna kallon yadda wata mota ta daga gidan kacokan zuwa sabon wuri

Wani bidiyon da ya bazu a kafafen sada zumuntar zamani na wani gida mai shekaru 139 ya bai wa jama'a mamaki.

Gidan da ke San Francisco an daga shi kacokan idan aka sauya masa unguwa.

Wani ma'abocin amfani da kafar sada zumuntar zamani ta Twitter mai suna @jrstonelive ya wallafa bidiyon.

An ga jama'ar yankin suna kallon yadda aka daga tsohon gidan daga lamba 807 Franklin St zuwa 635 Fulton St, San Francisco.

Hotuna da bidiyon yadda aka daga gida kacokan daga wata unguwa zuwa wata a Amurka
Hotuna da bidiyon yadda aka daga gida kacokan daga wata unguwa zuwa wata a Amurka. Hoto daga @jrstonelive
Source: Twitter

KU KARANTA: Nasara daga Allah: Sojin Najeriya sun tarwatsa nakiyoyin da Boko Haram suka sa a Marte

Hotuna da bidiyon yadda aka daga gida kacokan daga wata unguwa zuwa wata a Amurka
Hotuna da bidiyon yadda aka daga gida kacokan daga wata unguwa zuwa wata a Amurka. Hoto daga @jrstonelive
Source: Twitter

Kamar yadda ya wallafa, gidan ana sauya masa wuri ne kuma gida ne mai tsananin tarihi.

KU KARANTA: Dalilin da yasa ba za a yi wa kananan yara riga-kafin korona ba, Jami'i

Jama'a da dama sun dinga mamakin wannan cigaban da aka samu na daukar ginannen gida daga wani wuri zuwa wani wuri.

A wani labari na daban, wata budurwa mai amfani da @MrsKaranu a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter ta mika tayin soyayyarta ga saurayi a watan Yunin 2020 kuma ta aure shi babu dadewa.

A watan Yunin 2020, ta wallafa cewa ta mika tayin soyayyarta. Ta ce: "Yanzun nan na tashe shi. Ubangiji yayi min taimako!!!"

Bayan watanni kadan, budurwar ta koma kafar sada zumuntar zamanin ta Twitter ta kara da bayanin cewa "A yanzu mun yi aure".

Babu bata lokaci jama'a suka dinga yi mata Allah sam barka da wannan sa'ar da ta samu.

Ba kowacce mace bace ke samun sa'a kamar yadda kyakyawar budurwar ta samu ba. Wasu na nuna soyayyarsu kuma basu samu a so su.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel