Da duminsa: FG za ta fara shari'a da mutum 5,000 da ake zargi da ta'addancin Boko Haram
- Gwamnatin tarayya ta shirya tsaf domin fara shari'ar wadanda ta kama da zargin 'yan Boko Haram ne
- Daraktan kungiyar shari'ar wanda sune lauyoyi masu kare wadanda ake zargin, Aliyu Abubakar ya bayyana hakan
- Gwamnan jihar Borno, Farfesa Zulum ya ce ya shirya tsaf domin bai wa gwamnatin tarayya goyon bayan cimma manufarta
Gwamnatin tarayya ta ce nan babu dadewa za ta fara shari'ar wasu mutum 5,000 da ake zargi da zama 'yan ta'addan Boko Haram kuma suna tsare a gidajen gyaran halin kasar nan.
Darakta janar na kungiyar shari'a, Aliyu Abubakar, ya bayyana hakan a wata ziyara da ya kaiwa gwamnan Borno, Babagana Zulum a gidan gwamnati da ke Maiduguri.
Abubakar ya bayyana barikin Giwa da ke Maiduguri, gidan gyaran hali na Kainji a matsayin wuraren da aka adana wadanda ake zargin da ta'addanci, Daily Trust ta ruwaito.
KU KARANTA: Da duminsa: Sojojin Najeriya sun kwato garin Marte daga hannun Boko Haram
Ya ce za a fara shari'ar ne daga ofishin antoni janar na tarayya, ofishin mai bada shawara kan tsaron kasa tare da hadin guiwar rundunar Operation Lafiya Dole.
Ya yi bayanin cewa kungiyar taimako ta shari'ar ta tattauna da mutum 283 wadanda ake zargi duk a kokarinsu na fahimtar yanayin laifinsu.
"A matsayinmu na lauyoyin masu kare wadanda ake zargi, dole ne mu tattauna da su lokaci bayan lokaci domin mu san labarinsu. Ko da zarginsu ake yi, akwai yuwuwar a samu wadanda basu da laifi a ciki," yace.
Abubakar ya jinjinawa shugabancin Operation Lafiya Dole da ta samar da lauyoyi ga duk wadanda ke gidajen gyaran hali.
Gwamna Zulum ya ce a shirye yake da hada kai da gwamnatin tarayya domin bata damar cimma manufarta.
KU KARANTA: Tsuleliyar budurwa da ta nemi soyayyar matashi ta aure shi bayan watanni
A wani labari na daban, rahotanni sun nuna cewa dakarun sojin kasar Najeriya sun tarwatsa wasu nakiyoyi da Boko Haram suka saka a hanya mai zuwa Marte ta jihar Borno a matsayin tarkon halaka sojoji.
Hakan yana zuwa ne kasa da sa'o'i 48 bayan babban hafsan sojan kasa, Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya bai wa dakarun wa'adain kwato Marte daga hannun mayakan ta'addancin.
Kamar yadda jaridar PRNigeria ta bayyana, banda manyan nakiyoyin da Boko Haram suka saka, 'yan ta'addan sun saje da farar hula a Marte don hana soji kai musu harin bama-bamai ta jiragen yaki.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng