Hotunan kyakyawar likita da jama'a ke cewa kyanta da murmushinta za su iya warkarwa

Hotunan kyakyawar likita da jama'a ke cewa kyanta da murmushinta za su iya warkarwa

- Wata kyakyawar matashiyar budurwa ta zama abun kwatance bayan zamanta cikakkiyar likita

- Budurwa mai amfani da @__Marryaam ta wallafa kyawawan hotunanta uku sanye da kayan likitoci

- 'Yan Najeriya sun dinga magana a kan irin kyan da Allah ya zuba mata domin sun ce hakan zai iya warkar da marasa lafiya

Wata budurwa 'yar Najeriya ta kammala digirinta inda ta zama cikakkiyar likita kuma ta sanar da hakan cike da farin cikin wannan nasarar.

Babu kakkautawa kuwa ta wallafa hotunanta har uku a shafinta na Twitter mai suna @__Marryaam sanye da kayan likitoci.

"Daga bisani, na zama cikakkiyar likita... an dauka hoton da waya kirar iPhone 13," ta wallafa.

KU KARANTA: Tsuleliyar budurwa da ta nemi soyayyar matashi ta aure shi bayan watanni

Likita 'yar Najeriya da jama'a ke cewa kyanta da murmushinta za su iya warkarwa
Likita 'yar Najeriya da jama'a ke cewa kyanta da murmushinta za su iya warkarwa. Hoto daga @_Marryaam
Asali: Twitter

Tuni dai jama'a suka dinga tururuwar taya ta murna tare da mata fatan alheri amma kyanta ne ya fi komai jan hankulansu kuma yasa suka dinga tsokaci.

Masu tsokacin sun ce za su so zama marasa lafiyan da za ta duba ko don su cigaba da kallon kyakyawar fuskarta.

Wasu kuwa cewa suka yi murmushinta kadai ya isa ya warkar da mara lafiya daga dukkan cutukan da ke jikinsa.

KU KARANTA: Tsohon shugaban DSS ya bayyana inda Gumi ya gana da 'yan bindigan Neja

Ga wasu daga cikin tsokacin da Legit.ng ta tattaro:

@Mr2unechiSam ya ce: "Anya marasa lafiya za su dinga warkewa? Kada ki yi min fahimta ba daidai ba. Ba ina cewa baki kware bane ko wani abu. Ta yaya zan so dena ganin fuskar ki. Ina da tabbacin cewa kina da kamshi mai gamsarwa."

@MassageDoctor1 cewa yayi: "Wayyo! Da wannan kyan naki ji nake tamkar in dauke ki a matsayin likitata. Kyakyawar fuskar ki kadai da murmushin ki za su iya fatattakar ciwo."

A wani labari na daban, gwamnatin Najeriya ta yi bayanin cewa yara a kasar nan ba za a yi musu riga-kafin cutar korona ba koda ta iso Najeriya, Premium Times ta wallafa.

Daraktan hukuman NPHCDA, Faisal Shuaib yayin jawabin mako-mako na kwamitin fadar shugaban kasa ya ce ba a tabbatar da ingancin riga-kafin a kan kananan yara ba.

"Abinda aka sani shine an gwada riga-kafin Pfizer BioNTech ne a kan yara masu sama da shekaru 16 da kuma na Oxford- AstraZeneca a kan yara masu shekaru 18 zuwa sama," Shuaib yace.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel