Kagara: Dogo-Gide, shugaban 'yan bindiga ya tuntubi iyayen yara a kan kudin fansa

Kagara: Dogo-Gide, shugaban 'yan bindiga ya tuntubi iyayen yara a kan kudin fansa

- Shugaban 'yan bindigan Neja, Zamfara da Birnin Gwari, Dogo-Gide, ya tuntubi iyayen yaran Kagara

- Ya kira su ne bayan mako daya da kwashe yaran makarantar Kagara inda ya bukaci kudin fansa

- Duk da gwamnatocin tarayya da na jihar Neja suna cewa suna sasanci da 'yan bindigan kuma za a sako yaran

Bayan mako daya da yin garkuwa da yara maza na kwalejin kimiyya da ke Kagara a jihar Neja, wadanda ake zargi da garkuwa da mutane sun bukaci cinikin kudin fansa da iyayen yaran.

Wannan cigaban ya ci karo da matsayar gwamnatocin tarayya da na jiha na cewa suna sasanci da 'yan bindigan kuma akwai yuwuwar a sakosu babu dadewa.

Wanda ake zargin shugaban masu garkuwa da mutanen yayi magana da wakilin iyayen a wata na kusan mintuna takwas a ranar Litinin.

KU KARANTA: Mun zuba soyayya da mijin yayata, yanzu haka ya dirka min ciki, Budurwa na son shawara

Kagara: 'Yan bindiga sun fara bukatar kudin fansa daga hannun iyayen yara
Kagara: 'Yan bindiga sun fara bukatar kudin fansa daga hannun iyayen yara. Hoto daga @Vanguardngrnews
Asali: Twitter

An gano cewa ya bada sharadin da zai kawo karshen hauhawar ta'addanci a karamar hukumar Rafi, inda Kagara take.

Majiyoyin da suka zanta da Premium Times a kan wannan cigaban sun bayyana cewa shugaban 'yan bindigan mai suna Dogo Gide ne suka zanta da iyayen yaran.

Sun kwatanta Gide da shugaban 'yan bindigan da ke barna a Neja, Zamfara da Birnin Gwari ta jihar Kaduna.

Majiyoyin sun ce wanda ake zargin ya tabbatar da cewa shine ya jagoranci fashin wani banki a shekarar da ta gabata a Kagara kuma ya bukaci a watsa kungiyar 'yan sa kai a matsayin sharadin zaman lafiya.

KU KARANTA: Da duminsa: Sojojin Najeriya sun kwato garin Marte daga hannun Boko Haram

A wani labari na daban, tsohon mataimakin daraktan hukumar tsaro ta farin kaya, Dennis Amachree a ranar Litinin ya yi bayanin cewa jami'an tsaron da aka bai wa umarnin ceto yaran Kagara basu yi musayar wuta da su bane saboda gudun rasa rayuka.

Amachree wanda ya sanar da hakan a hirar da aka yi da shi a Channels TV ya ce 'yan bindigan za su iya yin garkuwa da mutanen da ke hannunsu idan jami'an tsaro suka bude musu wuta.

Ya kara da cewa fitaccen malamin, Sheikh Ahmad Gumi, ya hadu da 'yan bindiga a dajin Neja domin tattaunawa kan sakin malamai da daliban kwalejin kimiyya ta Kagara a kusa da wurin zaman sojoji, Daily Trust ta wallafa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel