Yan bindiga: Ƙungiyar Arewa ta juyawa Gumi baya, ta ce ya je ya ƙwaci kansa

Yan bindiga: Ƙungiyar Arewa ta juyawa Gumi baya, ta ce ya je ya ƙwaci kansa

- Kungiyar dattawan arewa ta nesanta kanta daga wasu kalamai na Sheikh Gumi

- Ta kuma bayyana cewa ya zama dole kungiyoyin arewa su fito su yi watsi da wadannan kalamai nasa don kada a yi zaton su yake ciwa albasa

- Hakan ya biyo bayan furucin da Gumi yayi na ikirarin cewa 'yan bindigar sun fusata saboda sojoji wadanda ba Musulmi ba ne ke kashe su

Kungiyar dattawan Arewa a ranar Laraba sun nesanta kansu daga maganganun kwanan nan da aka alakanta da malamin addinin Musulunci, Sheikh Abubakar Gumi, wanda ya zama jakadan sulhu da ’yan fashi a dazuzzukan da ke fadin jihohin Kaduna, Zamfara, Katsina, da Neja.

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa a yayin daya daga cikin irin wadannan tarurrukan, ya yi zargin cewa sojoji wadanda ba Musulmi ba sun aiwatar da kisan gilla a wasu garuruwa, lamarin da ya fusata su.

KU KARANTA KUMA: Abun mamaki: Hotunan yarinya ƴar firamare tana gyaran motoci ya jawo cece kuce a yanar Gizo

Yan bindiga: Dattawan Arewa sun barranta daga wasu kalamai na Sheikh Gumi
Yan bindiga: Dattawan Arewa sun barranta daga wasu kalamai na Sheikh Gumi Hoto: Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi
Asali: Facebook

"Abin da nake so ku fahimta shi ne, sojojin da ke da hannu a cikin yawancin laifukan ba Musulmi ba ne. Ku sani, sojoji suna da musulmai kuma suna da wadanda ba musulmai ba. Wadanda ba Musulmai ba ne ke haifar da rudani don kawai a haddasa rikici,” in ji Gumi.

Ya fadi hakan ne ga wata tawaga karkashin jagorancin Sakataren Gwamnatin Jihar Neja a kan aikin sulhu don sakin daliban Kagara da aka sace.

Amma dattawan da ke karkashin kungiyar Dattawan Arewa maso Gabas kan ci gaban Zaman Lafiya (NEEPD) sun ce zargin na Gumi bai wakilci matsayin yankin ba , suna masu cewa dole ne jama'a su yi wa abun kallo a matsayin "ra'ayin kansa".

Yayinda take kira ga jama'a da suyi watsi da wannan zargi, kungiyar ta NEEPD a cikin wata sanarwa daga jagoranta, Zana Goni, ta sha alwashin yin watsi da duk wani yunkuri na mutum ko wata kungiya kan sojin.

A cewarsu, ya zama dole manyan kungiyoyin Arewa su yi Allah wadai da ikirarin Gumi mai hadari, don kada mutane suyi tunanin cewa yana magana ne da yawun yankin.

KU KARANTA KUMA: An kori budurwa daga aiki a ranar farko saboda ta ce tana sha'awar manajan kamfanin

Duba ga kalaman nasa, ta iya yiwuwa Gumi na kare fashi da makami ne da duk abin da ke da nasaba da laifin.

A gefe guda, babban shehin malamin nan Ahmad Gumi ya bayyana cewa ƴan bindiga ba ƴan ta’adda ba ne domin faɗansu; “faɗan cikin gida”.

Ya dai yi wannan lafazi ne a wata hira da yayi da gidan wani talabijin a ranar Litinin inda ya tabbatar da cewa ƴan bindigar ba sa sha’awar kisan mutane, kuma ko da ƴan kaɗan ɗin da suka kashe, sun yi ne ba a bisa son ransu ba.

A wasu jihohi dai na Arewa maso yamma da kuma Arewa maso tsakiyar ƙasar nan, ana ta fama da cigaba da samun hare-hare na ƴan bindiga waɗanda ke zagayawa ƙauyuka suna kai farmaki a yayin da ba sa kan hanyoyi kamar yadda suka saba domin sace matafiya.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng