An kori budurwa daga aiki a ranar farko saboda ta ce tana sha'awar manajan kamfanin

An kori budurwa daga aiki a ranar farko saboda ta ce tana sha'awar manajan kamfanin

- Wata budurwa ta haddasa cece-kuce a shafin soshiyal midiya bayan an kore ta daga aiki a ranar farko kan maganar da tayi wa manajan ta

- Budurwar wacce ba a san kowacece ba ta gaya wa manajan ta cewa yana da kyau kuma ta tambaye shi ko 'za ta iya zama a fuskarsa'

- Da yake bayyana hakan a shafinsa na Twitter, jagoran ci gaban kamfanin Dipo Awojide ya ce nan ba da dadewa ba kamfaninsa zai tallata aikin budurwar

An kori wata 'yar Najeriya a ranar farko da ta fara aiki bayan ta tambayi manajan nata idan 'zata samu damar kebewa da shi kuma za ta iya zama a fuskarsa' a ranarta ta farko a wajen aiki.

Jagoran ci gaban kamfanin Dipo Awojide ne ya bayyana hakan a shafin soshiyal midiya.

KU KARANTA KUMA: Gumi ya koma limamin ƴan bindiga, ya kamata a tuhume shi, cewar wata ƙungiyar Arewa

An kori budurwa daga aiki a ranar farko saboda ta ce tana sha'awar manajan kamfanin
An kori budurwa daga aiki a ranar farko saboda ta ce tana sha'awar manajan kamfanin Hoto: Maciej Luczniewski/NurPhoto
Asali: Getty Images

A kalamansa:

"Ta yaya zaki je ki tambayi manajanki namiji cewa " kana da kyau sosai, shin zan iya samun kebewa da kai? Shin zan iya zama a fuskarka" a ranar farko da fara sabon aikinki? Wasu daga cikinku suna da ƙarfin hali amma sai su tsinci kansu a wahala mara dalili. Shin ba kwa son aikinku? Yanzu HR ta shiga ciki."

A cewar Awojide, za a biya matar da ake magana a kanta kudin aiki na kwana daya bayan an kore ta. Ya kuma bayyana cewa kamfaninsa zai tallata aikin yarinyar nan ba da dadewa ba.

'Yan Najeriyar sun yi mamakin kalaman matar kuma ba da daɗewa ba suka cika sashen sharhi na rubutun Awojide don su bayyana ra'ayinsu a kai.

@ogunbiyiseyi1 yayi tsokaci:

"Wani lokacin idan mace na da kyau sai ta zaci dama ce ta kaiwa ga duk mutumin da take so, lol ba haka bane, kuma ba kowa bane zaki iya ruda da kyanki, kawai karfin gwiwa ne yake zuwa har kiyi tunanin babu wanda zai iya kin ki saboda kawai kina da kyau."

KU KARANTA KUMA: Bankwanan ADC da Buhari: Ƙaramar yarinya ta nuna bajinta, ta sarawa shugaban ƙasa

@Bintz001 yayi sharhi:

"Ka yi tunanin idan da namiji ne ya tunkari mace da irin wannan bayanin. Da Twitter NG ya yi wa dukkanmu kadan a yau ..."

A wani labari, wata budurwa 'yar Najeriya ta kammala digirinta inda ta zama cikakkiyar likita kuma ta sanar da hakan cike da farin cikin wannan nasarar.

Babu kakkautawa kuwa ta wallafa hotunanta har uku a shafinta na Twitter mai suna @__Marryaam sanye da kayan likitoci.

"Daga bisani, na zama cikakkiyar likita... an dauka hoton da waya kirar iPhone 13," ta wallafa.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng