Dalilin da yasa ba za a yi wa kananan yara riga-kafin korona ba, Jami'i

Dalilin da yasa ba za a yi wa kananan yara riga-kafin korona ba, Jami'i

- Gwamnatin Najeriya ta ce ba za ta yi wa kananan yara riga-kafin cutar korona ba

- Kamar yadda ta bayyana, an gwada ingancin riga-kafin ne a kan masu shekaru 18 zuwa sama ne

- An gwada riga-kafin Pfizer BioNTech kan masu shekaru 16 zuwa sama, na Oxford- AstraZeneca kan masu shekaru 18

Gwamnatin Najeriya ta yi bayanin cewa yara a kasar nan ba za a yi musu riga-kafin cutar korona ba koda ta iso Najeriya, Premium Times ta wallafa.

Daraktan hukuman NPHCDA, Faisal Shuaib yayin jawabin mako-mako na kwamitin fadar shugaban kasa ya ce ba a tabbatar da ingancin riga-kafin a kan kananan yara ba.

"Abinda aka sani shine an gwada riga-kafin Pfizer BioNTech ne a kan yara masu sama da shekaru 16 da kuma na Oxford- AstraZeneca a kan yara masu shekaru 18 zuwa sama," Shuaib yace.

KU KARANTA: Saboda mata: ISWAP da bangaren Shekau anyi artabu, an sheke 'yan ISWAP masu tarin yawa

Dalilin da yasa ba za a yi wa kananan yara riga-kafin korona ba, Jami'i
Dalilin da yasa ba za a yi wa kananan yara riga-kafin korona ba, Jami'i. Hoto daga @Premiumtimes
Asali: Twitter

"Abinda muka sani shine wadannan jerin mutanen sune kadai aka gwadawa riga-kafin."

Ya ce har yanzu ana bincike a kan illar da Covid-19 ke yi wa kananan yara.

"Amma kuma daga bayanan da NCDC ta sanar, cutar korona ta fi gallabar manya da masu shekaru masu yawa, ballantana tsofaffi," yace.

Najeriya za ta samu riga-kafin korona miliyan hudu na kamfanin Oxford-AstraZeneca a cikin kwanakin nan.

Gwamnati ta ce tana da burin yi wa kusan 109 milliyan riga-kafin cutar a cikin shekaru biyu.

KU KARANTA: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da dagaci a jihar Katsina

A wani labari na daban, wasu makasan haya sun bindige Okiemute Sowho, wani hadimin gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa.

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, an kashe Sowho a yammacin Asabar, 20 ga watan Fabrairun 2020 a garin Sapele da ke jihar Delta.

Legit.ng ta gano cewa, har zuwa rasuwar mamacin, shine hadimi na musamman a harkar cigaban matasa ga Gwamna Okowa.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng