Tsuleliyar budurwa da ta nemi soyayyar matashi ta aure shi bayan watanni

Tsuleliyar budurwa da ta nemi soyayyar matashi ta aure shi bayan watanni

- Wata matshiyar budurwa ta tabbatar da cewa mai nema baya rasawa domin ta kai tayin soyayyarta kuma ta yi sa'a

- Budurwa mai amfani da @MrsKaranu a Twitter ta bayyana yadda ta sanar da wani saurayi tana son sa kuma ta aure shi

- Bayan watanni kadan da wallafar, sai ga kyawawan hotunan aurenta da matashin sun bayyana inda take cike da murna

Wata budurwa mai amfani da @MrsKaranu a kafar sada zumuntar zamani ta Twitter ta mika tayin soyayyarta ga saurayi a watan Yunin 2020 kuma ta aure shi babu dadewa.

A watan Yunin 2020, ta wallafa cewa ta mika tayin soyayyarta. Ta ce: "Yanzun nan na tashe shi. Ubangiji yayi min taimako!!!"

Bayan watanni kadan, budurwar ta koma kafar sada zumuntar zamanin ta Twitter ta kara da bayanin cewa "A yanzu mun yi aure".

KU KARANTA: Boko Haram: 'Yan ta'adda sun kafa tutocinsu a Marte, daruruwan jama'a sun shiga sarkakiya

Tsuleliyar budurwa da ta nemi soyayyar matashi ta aure shi bayan watanni
Tsuleliyar budurwa da ta nemi soyayyar matashi ta aure shi bayan watanni. Hoto daga @MrsKaranu
Asali: Twitter

Babu bata lokaci jama'a suka dinga yi mata Allah sam barka da wannan sa'ar da ta samu.

Ba kowacce mace bace ke samun sa'a kamar yadda kyakyawar budurwar ta samu ba. Wasu na nuna soyayyarsu kuma basu samu a so su.

Ga martanin jama'a ga budurwar mai sa'a.

Jama'a sun bisu suna ta yi musu fatan zaman lafiya tare da zuria tagari.

KU KARANTA: Kyawawan hotunan zukekiyar 'yar gwamnan Bauchi yayin da ta zama cikakkiyar likita

A wani labari na daban, taron kungoyoyi masu zaman kansu guda 43 sun bukaci shugaba Muhammadu Buhari yayi murabus tunda ya gaza kawo karshen rashin tsaro a kasar nan.

Sun bayyana hakan ne a wani taro da suka yi a Abuja jiya, Daily Trust ta ruwaito.

A cikin bukatunsu har da samar da shugabanci na kwarai sannan gwamnati ta baiwa jama'a tallafi kamar yadda bangare na 17 (2) (C) na kundin tsarin mulki ya tanadar.

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel