Jarumar fim din Dadin Kowa: Burina Nollywood da Kannywood su hada kai, in ji Stella
- A wata hira da gidan jarida, Stella jarumar fim din Dadin Kowa ta bayyana ko wacece ita
- Ta kuma bayyana kalubale, ci gaba da halin da harkar fim na Kannywood ke ciki a yanzu
- Hakazalika ta bayyana burinta na hade tsakanin Nollywood da Kannywood a inuwa daya
Beatrice Williams Auta, ‘yar fim din Kannywood da ta taka rawa a matsayin Stella a cikin shirin Arewa24 'Dadin Kowa’, ita ce mai jin daɗin hira kowane rana. A tattaunawa da Aminiya, jarumar ta bayyana abubuwa masu ban sha'awa game da kanta.
Ta yi magana kan girma, makarantun da ta yi karatu, rayuwarta ta sirri da kuma abubuwan da za ta sauya a masana'antar finafinan Hausa idan tana da iko.
Ta kuma mayar da martani game da zargin da ake yi cewa akwai 'yan luwadi da madigo a Kannywood sannan ta bayyana wasu kalubalen da ta ke fuskanta a masana'antar. Ji dadin hirar.
KU KARANTA: Tsadar kudin wutan lantarki: Muna biyan ninki ukun abinda muke biya a baya, 'yan Najeriya
Za ki iya gaya mana ko ke wacece?
Sunana Beatrice Williams Auta, wacce aka fi sani da Stella Dadin Kowa. Ni haifafiyar garin Kaduna ne kuma anan na tashi, amma asali iyaye na sun fito daga jihar Taraba ne.
Na yi Makarantun Firamare da Sakandare a Kaduna kuma na yi karatun Turanci da wasan kwaikwayo a Jami'ar Jihar Kaduna. Mu biyu mata iyaye na suka haifa. Mahaifina ya rasu amma mahaifiyata tana raye.
Me ya ja hankalinki zuwa masana’antar finafinan Hausa?
To, na zabi fim din Hausa ne saboda ni 'yar arewa ce kuma mai magana da harshen Hausa. Na zabi fim din hausa ne don nishadantar, fadakarwa, da kuma ilimantar da mutane ta wannan yaren.
Lokacin da nake ƙarama, Ina son finafinan Indiya. Har zuwa yau, ina son rawarsu, soyayya da komai. Kuma idan ka kalli finafinan Hausa, za ka ga yadda suke daukar al'adun Indiya. A arewa, muna da al’adun da aka tanada, shi ya sa na zabi farawa da fina-finan Hausa.
Yaushe kika fara fitowa a fim?
Na fara fitowa a fina-finan Hausa ne a shekarar 2017.
Wanne ne fim dinki na farko?
Na farko kuma da na fi so shi ne ‘Dadin Kowa’
Zuwa yanzu fina-finai nawa kika fito a ciki?
Ina tsammanin ya zuwa yanzu, na fito a cikin fina-finai tsakanin 10 zuwa 15.
Kina da aure?
Gaskiyar ita ce, ko ma menene, ba na magana game da rayuwata a cikin jama'a. Da fatan za mu ci gaba zuwa tambaya ta gaba?
A masana'antar, su wa suka fi burgeki?
Bari na fara da cewa ina kaunar Adam A. Zango, Ali Nuhu, kuma a jarumai mata da nake so su ne Rahama Sadau da Nafisa Abdullahi.
Kwanan nan, an samu rikice-rikice da yawa a Kannywood, me kuke ganin yake da alhakin wannan rikici?
To, ina tsammanin Kannywood ta fuskanci rikice-rikice da yawa saboda an yi watsi da bangaren kwarewa.
Wannan na iya zama saboda kudade; ba abu ne mai sauki ba don samun ingantattun kayan aiki don samarwa aikin. Hakanan, 'yan wasan da aka fitar bisa lafazin ra'ayi na bangaranci, babu kwarewar aiwatar da fim, don haka ina ganin wannan na daga cikin dalilan hakan.
Kina daya daga cikin manyan jarumai a cikin ‘Dadin Kowa’, fim mai matukar nasara, amma ba zato ba tsammani kika bace, shin akwai wani dalilin hakan?
Eh. Na bace amma ban san dalilin da yasa na bace ba; babu wani dalili da zai zama daidai. Ban sani ba ko zan sake bayyana.
Akwai rade-radin cewa wasu daga cikin ‘yan wasan fim din 'Dadin Kowa' sun samu sabani da gudanarwa ta Arewa24, kuma wannan ya sa aka cire su daga jerin, me za ki ce kan hakan?
Kamar yadda kuka fada, jita-jita ce. Ba zan iya magana game da wasu ba sai dai karan kaina.
A gaskiya ba ni da wata matsala game da fannin gudanarwar ‘Dadin Kowa’ amma ba zan iya cewa ga wasu ba. Zai yuwu cewa fannin gudanarwa tana da matsala dani, amma ban taba samun matsala da kowa ba saboda ko yaushe ina yin abin da suke so.
KU KARANTA: Farashin man fetur zai iya cillawa zuwa N200, sakamakon tashin farashin danyen mai zuwa $64
"Wataƙila masu gudanarwar sun sami matsala dake?" Shin za k iya yin karin bayani kan hakan?
Na ce watakila, ban tabbata ba saboda a masana'antar wani na iya yanke shawarar ba ya son ka a dabi'ance, kuma wani na iya yanke shawarar son ka kuma ya fifita ka. Don haka, ban ce akwai wani batun ba. Ina cewa watakila amma ban sani ba gaskiya.
Shin kina ganin siyasa ta taka rawa a rikicin da aka samu tsakanin fitattun jaruman Kannywood?
Yawancin rikice-rikice da kuke gani a cikin kowace al'umma suna da alaƙa da siyasa. Siyasa wasa ne na sha'awa kuma masana'antar tana da bangarori da yawa da ke da sha'awa iri daban-daban.
Akwai wani zargi da ake yi cewa wasu taurari a Kannywood ‘yan luwadi ne/madigo, me za ki ce game da wannan?
Ka ce jita-jita da jita-jita sune abin da za ka iya ji amma ba ka gani ba. Don haka na kasance ina jin abu guda amma ban hadu da komai ba, don haka babu wani abu makamancin haka a gare ni.
Shin ko kina fuskantar wani kalubale a masana'antar sakamakon rashin kasancewar ki bahaushiya?
Eh na fuskanci kalubale.
Waɗanne ƙalubale ne?
Na farko shi ne addini, sannan kabilanci. Saboda wasu daga cikin furodusoshin sun yi imanin idan ba ainihin bahaushe ba ne, ba za ka iya fassara ko ba su abin da suke so ba.
Kamar dai akwai wani takamamman Hausa wanda aka fi amfani dashi a Kannywood. Duk da cewa dukkanmu 'yan arewa ne, suna jin akwai wani mizani na hausa wanda dole sai anyi shi. Ina tsammanin waɗannan manyan matsaloli ne.
Shin zaka iya auren wani a cikin Kannywood?
Ee, ba shakka. Zan iya, ina tsammanin wannan zai sanya kyakkyawar haɗuwa.
Ko akwai wanda ya riga ya?
Wannan sirri ne. Lokacin da lokaci yayi, zaku sani.
Za ki iya ba mu alamar gane saurayin?
Eh to, yana da tsayi sosai, wannan alama ce?
Idan kina da ikon gyara matsala a cikin Kannywood, menene zaki gyara?
Da fari dai, zan inganta hadin kai a masana'antar. Hadin kai tsakanin furodusoshi, 'yan wasan kwaikwayo, daraktoci da sauransu.
Abu na biyu, haɗin kai da wasu, ina nufin waɗanda ke cikin Nollywood, kuma wannan yunkurin ne don sanya finafinanmu su wuce inda suke a yanzu.
Abu na uku, Zan tabbatar da cewa mun shirya karin horo ga 'yan wasanmu da ma'aikatanmu, ta yadda za mu iya gogayya da fina-finan kasashen waje. Gaskiya, muna da labarai masu kyau da wurare masu kyau.
Menene babban burin ki a Kannywood?
Ina gina kaina da aikina. Nan ba da dadewa ba zan fara samar da wani sabon aiki, da yardar Allah, zan bunkasa ta wannan hanyar kuma in zama babbar 'yar wasan Kannywood.
A wani labarin, Mata a yanzu za su iya shiga cikin rundunar sojan Saudiyya, bayan hukuncin da Ma’aikatar Tsaro ta Saudiyya ta yanke wanda ya bude wa dukkan mata da maza damar yin rajista ta wata babbar hanyar shiga daga ranar Lahadi.
Matsayi na soja daga soja zuwa sajan zai kasance a cikin Sojojin Saudi Arabiya, Royal Saudi Air Defense, Royal Saudi Navy, Royal Saudi Strategic Missile Force, da Fannin Kiwon Lafiyar Sojoji, Arab News ta ruwaito.
Salisu Ibrahim, mai rubutu a masana'antar Legit.ng Hausa da ya fara aiki a baya-bayan nan. Ya kware wajen kawo rahotanni na siyasa, kimiyya, al'adu da sauran lamurran yau da kullum.
Ya yi karatun diploma a fannin karantar da turanci a jami'ar Ahmadu Bello, ya kuma karantar na tsawon shekaru 7.
A halin yanzu yana zangon karshe na karatun digiri a fannin ilimin fasahar sadarwa a International Open University.
Ku bibiyi shafinsa na twitter a @therleez
Asali: Legit.ng