Gwamnatin Tarayya ta san inda ‘Yan bindiga su ke boyewa inji Sheikh Ahmad Gumi

Gwamnatin Tarayya ta san inda ‘Yan bindiga su ke boyewa inji Sheikh Ahmad Gumi

- Ahmad Gumi ya maida martani ga masu tambayar yadda yake ganin ‘Yan bindiga

- Shehin Malamin ya ce Gwamnatin Tarayya ma ta san inda wadannan miyagu suke

Fitaccen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi, ya ce gwamnatin tarayya ta san inda miyagun ‘yan bindiga su ke buya.

Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya ce gwamnatin Najeriya tana da ilmin inda wadannan miyagu da su ke kashe-kashe da garkuwa da mutane su ke.

Malamin musuluncin yake cewa gwamnati ta na bi sannu hankali ne kurum saboda ta gano cewa kai wa ‘yan bindigan hari gaba-da-gaba bai da riba.

Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi wannan jawabi ne a gidan Channels TV, lokacin da aka yi hira da shi a shirin ‘Politics Today; a ranar Litinin dinnan.

KU KARANTA: Kagara: Dalibai 27 da Ma’aikata 15 su na tsare a hannun ‘Yan bindiga

Shehin ya maida martani ne ga tambayar da aka yi masa na cewa ya aka yi yake zama da ‘yan bindigan nan, a lokacin hukuma ba su iya kai wa gare su.

"Su (Gwamnati) sun sani. Su na ganinsu (miyagun) ta jiragen sama. Amma sojoji sun yi hankali ne"

“Da farko dabarar da su ka yi ita ce, sun je sun fara kashe su, sai su ka gano hakan ba zai yiwu ba. Yanzu sun yi hattara. Abin da na kara shi ne, na ce ayi sulhu.”

Amma Middle Belt Forum ta soki kiran da malamin yake yi na cewa a zauna da ‘yan bindigan. Kungiyar ta ce hakan ya zama ana saka wa miyagun da alheri.

Gwamnatin Tarayya ta san inda ‘Yan bindiga su ke boyewa inji Sheikh Ahmad Gumi
Dr. Ahmad Gumi Hoto: dailytrust.com
Source: UGC

KU KARANTA: Makiyaya sun mallaki AK-47 - Gwamnan Filato

Haka zalika sauran kungiyoyi irinsu Pan-Niger Delta Forum, Ohanaeze Ndigbo; da Afenifere duk sun yi tir da kiran shehin na cewa ayi wa ‘yan bindigan afuwa.

Wasu Kungiyoyi da-dama sun soki kokarin Ahmad Gumi na yin sulhu da ‘Yan bindiga. Niger Delta Forum, Ohanaeze Ndigbo; da Afenifere duk sun yi tir Gumi.

A jiya ne Gwamna Samuel Ortom na jihar Benuwai, ya ce abokin aikinsa, gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, za a kama idan har aka ji an hallaka shi.

Samuel Ortom ya yi kira ga takwaransa, Gwamna Bala Abdulqadir Mohammed ya nemi afuwar mutane a kan wasu kalamai da ya yi, ya na kare ta'adin makiyaya.

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai, kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel