Da duminsa: Makasan haya sun aike da hadimin gwamna lahira

Da duminsa: Makasan haya sun aike da hadimin gwamna lahira

- An harbe hadimi na musamman na gwamna Okowa a kan cigaban matasa, Okiemute Sowho

- An gano cewa makasan haya sun halaka mamacin a ranar Asabar, 20 ga Fabrairu da yammaci

- Rundunar 'yan sandan jihar Delta ta tabbatar da aukuwar lamarin a ranar Lahadi

Wasu makasan haya sun bindige Okiemute Sowho, wani hadimin gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa.

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, an kashe Sowho a yammacin Asabar, 20 ga watan Fabrairun 2020 a garin Sapele da ke jihar Delta.

Legit.ng ta gano cewa, har zuwa rasuwar mamacin, shine hadimi na musamman a harkar cigaban matasa ga Gwamna Okowa.

KU KARANTA: Saboda mata: ISWAP da bangaren Shekau anyi artabu, an sheke 'yan ISWAP masu tarin yawa

Da duminsa: Makasan haya sun aike da hadimin gwamna lahira
Da duminsa: Makasan haya sun aike da hadimin gwamna lahira.Hoto daga Governor Ifeanyi A. Okowa
Asali: Facebook

Wasu majiyoyi da suka bukaci a boye sunansu sun sanar da The Nation cewa akwai yuwuwar makasan haya ne domin kuwa basu dauka komai ba daga wurin mamacin.

An gagauta kai shi wani asibiti mai zaman kan shi inda likitoci suka tabbatar da mutuwarsa.

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Delta, Edafe Bright, ya tabbatar da aukuwar mummunan lamarin.

Har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, gwamnatin jihar Delta bata fitar da wata takarda ba a kan aukuwar lamarin.

KU KARANTA: Matukin jirgi ya yi korafin matsala a injin sa'o'i kadan kafin ya rikito daga sama

A wani labari na daban, sshe sojojin sama na NAF201 da suka yi hatsari a jirgin sama, har mutane 7 da matukan jirgi da suka mutu a Abuja, suna neman wadanda aka sace a Kagara ne, kamar yadda bayanai suka bayyana a ranar Lahadi da yamma.

Kamar yadda aka samu labari, bayan kara wa jirgin mai a Abuja, jirgin ya bazama neman 'yan makarantan Kagara da aka sace ne a jihar Neja, Vanguard ta wallafa.

"Jirgin ya nufi Abuja don shan mai, injin jirgin ya samu matsala yayin da ya keta hazo ya kasa sakkowa duk da kokarin da yayi don sauka lafiya."

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel