Kyawawan hotunan zukekiyar 'yar gwamnan Bauchi yayin da ta zama cikakkiyar likita
- Diyar gwamnan Bauchi, Sanata Bala Mohammed ta zama cikakkiyar likita
- An rantsar da ita a ranar 18 ga watan Fabrairun 2021 a shagalin bikin da aka yi
- Mahaifinta, mahaifiyarta tare da 'yan uwa da abokan arziki sun samu halarta
Dr. Hauwa Mohammed, diyar gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed na daga cikin likitocin da aka horar a kasashen ketare wadanda suka dawo gida Najeriya aka rantsar da su.
Hukumar likitoci da likitocin hakora ta Najeriya ce ta rantsar da su a ranar Alhamis, 18 ga watan Fabrairun 2021.
Shagalin bikin rantsar da su ya samu halartar gwamnan, matarsa Dr Hajiya Aisha Bala Abdulkadir Mohammed da sauran 'yan uwa da abokan arziki.
KU KARANTA: Jirgin da yayi hatsari yana neman yaran makarantan Kagara ne, Majiya
A cikin kwanakin nan Gwamna Bala Mohammed ya kasance a kanun labarai tun bayan da yayi martani ga takwaransa na jihar Ondo wanda ya umarci makiyaya da su bar jiharsa.
Hakan ne yasa takwaransa na jihar Ondo, Akeredolu ya gargadesa da kada ya tada yaki a kasar nan baki-daya.
Amma kuma daga bisani Sanata Mohammed ya ce kariya kawai yake fatan Fulanin suyi amma ba ta'addanci.
KU KARANTA: Attahiru ya ba sojin Najeriya sa'o'i 48 su kwato Marte daga hannun Boko Haram
Tuni gwamna Mohammed ya ce makiyaya suna da damar yawo da bindiga AK47 domin baiwa kansu kariya da shanunsu daga bata-gari da ke kai musu hari tare da sace shanunsu.
KU KARANTA: Jirgin da yayi hatsari yana neman yaran makarantan Kagara ne, Majiya
A wani labari na daban, gagarumar arangama tsakanin Boko Haram bangaren Abubakar Shekau da mayakan ISWAP ya kawo ajalin mayakan ISWAP masu tarin yawa, HumAngle ta ruwaito.
Gagarumin fadan ya faru ne a yankinsa tsakanin iyakar Nijar da Najeriya. Al-Thabat, wata kafar yada labarai mai alaka da al-Qaida ta bayyana.
A wata takarda da Al-Thabat ta fitar, ta ce Jama’at Ahl as-Sunnah lid-Da’wah wa’l-Jihad wacce aka fi sani da Boko Haram ta halaka mayakan ISWAP a wani kauye da ake kira da Sunawa tsakanin iyakar Najeriya da jamhuriyar Nijar.
Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.
Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.
Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa
Asali: Legit.ng