Jerin sunayen dakarun sojin sama da suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin sama

Jerin sunayen dakarun sojin sama da suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin sama

- Dakarun sojin saman bakwai ne suka rasa rayukansu sakamakon hatsarin jirgin sama

- An gano cewa matukin jirgin saman ya yi korafi a kan matsalar injin din jirgin kafin hatsarin

- Tuni dai shugaban dakarun sojin saman Najeriya ya bada umarnin bincike kan hatsarin

A kalla dakarun sojin saman Najeriya 7 ne suka rasa rayukansu bayan rikitowar jirgin sama da suka hau wanda ya tunkari garin Minna da ke jihar Neja.

An gano cewa an sanar da matsala a injin din jirgin wurin karfe 10:39 na safe amma sai ya tarwatse a yayin da yake sauka a Abuja wurin karfe 10:48 na safe.

Jirgin saman ya tarwatse ne bayan da ya doke wata itaciyar mangwaro, ganau ba jiyau ba suka tabbatar da hakan.

Jaridar Daily Trust ta samu jerin sunayen sojojin da suka rasa rayukansau sakamakon faduwar jirgin saman.

KU KARANTA: Gagarumar gobara ta lashe shaguna a kasuwar kayan gyaran motoci ta Kaduna

Jerin sunayen dakarun sojin sama 6 da suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin sama
Jerin sunayen dakarun sojin sama 6 da suka rasa rayukansu a hatsarin jirgin sama. Hoto daga @daily_trust
Asali: Twitter

Ga sunayen kamar haka:

1. Flt. Lt. Gazama

2. Flt. Lt. Piyo

3. Flg. Offr. Okpara

4. FS Olawumi

5. ACM Johnson

6. Sgt Oloka

Shugaban rundunar sojin saman Najeriya, Aire Vice Marshal Oladayo Amao ya bada umarnin binciken musabbabin wannan mummunan hatsarin.

KU KARANTA: Makiyaya basu bukatar izininka don zama a dajika, Gwamnan Bauchi ga Akeredolu

A wani labari na daban, matukin jirgin sojan sama na rundunar dakarun sojin sama da ya fadi a Abuja a ranar lahadi, ya yi korafin cewa injin jirgin yana da matsala kafin mintoci kadan da tashin shi.

Wata majiya ta sanar da hakan ga jaridar The Punch amma ya bukaci a adana sunansa.

Jami'in ya ce ana ta samun masu kaiwa da kawowa a jiragen sama daga Abuja zuwa Minna tun bayan sace yara da ma'aikatan makaranta a Kagara a makon jiya.

Majiyar ta ce, "Jirgin yana kan hanyarsa ta zuwa Minna. Bayan kankanin lokaci da isarsa karamar hukumar Bassa, ya sanar da cewa injin jirgin ya samu matsala.

"An shawarcesa da ya koma filin sauka da tashin jiragen sama da ke Abuja amma sai ya rikito daga sama."

Aisha Khalid ma'aikaciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018.

Ta kwashe shekaru biyu tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu.

Za a iya bibiyar Aisha a shafinta na Twitter @DiyarKatsinawa

Asali: Legit.ng

Online view pixel