Bidiyon sojojin Najeriya yayin da suka kwace gonar Shekau a dajin Sambisa

Bidiyon sojojin Najeriya yayin da suka kwace gonar Shekau a dajin Sambisa

- Dakarun rundunar sojojin Najeriya sun kai mamaya wata gona da ake zargin ta shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ce

- A cikin wani bidiyo da ya bayyana na sojojin, an jiyo su suna yi wa Shekau shagube a kan ya fito daga maboyarsa

- Hakazalika an gano wasu yan fararen hula suna kwasar amfanin gonar wacce ke a cikin dajin Sambisa

Dakarun sojojin Najeriya sun mamaye wata gona da ake zargin mallakar Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ce a dajin Sambisa.

A cikin wani bidiyo da jaridar PRNigeria ta saki, an gano yadda sojojin suka afka wa gonar tare da wasu yan fararen hula suna kwasar amfanin gona.

An jiyo sojojin suna yi wa shugaban yan ta’addan ba'a sannan suka nemi da ya fito daga inda ya buya.

KU KARANTA KUMA: Rashin tabbas yayin da lauya ya shigar da kara don hana majalisar dattawa tabbatar da sabon shugaban EFCC

Bidiyon sojojin Najeriya yayin da suka kwace gonar Shekau a dajin Sambisa
Bidiyon sojojin Najeriya yayin da suka kwace gonar Shekau a dajin Sambisa Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Sojojin sun ce: “Shekau ina kake sarkin ɓaɓatu, ga mu a gonarka za mu yi sallar Juma’a a cikin Sambisa.

“Ba ka ce za ka yi shahada ba, ka fito mu barar da kai.”

A halin da ake ciki, sojojin Najeriya a Dikwa bayan dakile harin da ISWAP suka yi, sun kama wasu maza biyu da ake zargi da yi wa 'yan ta'adda leken asiri a cikin al'umma.

Ga bidiyon a kasa:

KU KARANTA KUMA: ‘Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu mata 13 a jihar Katsina

A baya mun ji cewa Boko Haram, a ranar Juma'a, sun afka karamar hukumar Dikwa, inda suka rika harbe-harbe bayan fafatawa da jami'an tsaro, a cewar wasu majiyoyi.

Mazauna garin, ciki har da yan gudun hijira sun tarwatse suna neman inda za su tsira sakamakon karar abin fashewa da na harbin bindiga da ya mamaye garin, rahoton jaridar Vanguard.

A cikin wannan makon, wasu yan ta'addan sun afka karamar hukumar Marte sun tafka ta'adi inda suka kwace iko a garin suka kafa tutarsu a hedkwatar karamar hukumar.

Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai.

Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi.

Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara.

Don samun karin bayani a kan ta, ziyarci shafinta na Twitter @ AishaMu11512411

Asali: Legit.ng

Online view pixel